Ambaliya: Rundunar Sojoji ta Mika Ta'aziyya Borno, Za a Taimaka wa Jama'a

Ambaliya: Rundunar Sojoji ta Mika Ta'aziyya Borno, Za a Taimaka wa Jama'a

  • Rundunar sojojin kasar nan ta umarci dakarunta da ke jihar Borno su bayar da agajin da ake bukata wajen ceto al'umma
  • Umarnin ya zo bayan ambaliyar ruwa ya mamaye fiye da rabin Maiduguri, babban birnin Borno yayin da mutane suka makale
  • Babban hafsan tsaron, Janar Christopher Musa ya ce dakarunsu za su yi aiki kafada da kafada da kungiyar bayar da agaji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ba dakarun da ke Borno umarnin bayar da agajin da ya dace ga wadanda iftila'in ambaliya ya shafa.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Jami'an agaji sun maƙale a ruwa daga zuwa ceto mutane

A ranar Talata ne aka samu ballewar madatsun ruwa a Borno, wanda ya shanye gidaje, wuraren aiki, makarantu da tituna a Maiduguri.

Christopher Musa
Ambaliya: Dakarun soja za su taimaka wa jama'a a Maiduguri Hoto: Katsina State Government
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa babban hafsan sojojin ya taya jama'ar Borno, musamman na Maiduguri jimamin iftila'in da ya jefa jama'a cikin fargaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji za su bayar da agaji bayan ambaliya

Rundunar sojojin kasar nan ta bayyana cewa za ta yi aiki da hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA) domin taimaka wa wadanda ambaliya ta shafa.

Wannan na kunshe a sanarwar da daraktan yada labaran rundunar, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, inda ya ce an umarci dakarun su bayar da agaji.

Sojoji sun mika ta'aziyya saboda ambaliya

Baban hafsan tsaron kasar nan, Janar Christopher Musa ya mika ta'azziyya ga mutanen da su ka rasa yan uwansu bayan ambaliya ya wanke sashen Maiduguri.

Kara karanta wannan

Borno: Muhimman wurare 5 da ambaliyar ruwa ta fi yin barna a Maiduguri

Janar Christopher Musa ya kuma mika jaje ga dubban mutane su ka rasa muhallansu da dukiyoyinsu bayan fashewar madatsar ruwa ta Alo da ya haddasa mummunan ambaliya.

Ambaliya ta lalata garin Maiduguri

A baya kun ji yadda aka samu mummunan ambaliyar ruwa da aka shafe shekaru akalla 30 ba a ga irinta a Borno ba, lamarin da ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ambaliyar ta lalata fadar Shehun Borno, jami'ar Maiduguri (UNIMAID), gidan adana namun daji da sauran gidajen al'umma inda ruwa ya shanye gine-gine.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.