APC Ta Kwancewa Tinubu Zani a Kasuwa kan Tsadar Rayuwa
- Jam'iyyar APC ta mayar da martani kan kalaman da tsohon mataimakin shugabanta na ƙasa, Salihu Lukma ya yi
- APC ta amince cewa manufofin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu sun ƙara taɓarɓarar da tattalin arziƙin ƙasar nan
- Sai dai jam'iyyar ta bayyana cewa matakan da Tinubu ya ɗauka, ya ɗauke su ne domin farfaɗo da tattalin da ya durƙushe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta amince cewa manufofin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɓullo da su sun ƙara taɓarɓarar da tattalin arziƙin ƙasar nan.
Sakataren yaɗa labaran APC na ƙasa, Barista Felix Morka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
APC ta yi martani ga Salishu Lukman
Jaridar Daily Trust ta ce sakataren yaɗa labaran na APC ya mayar da martani ne ga tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa (Arewa maso Yamma) Salihu Mohammed Lukman.
Salihu Lukman dai ya zargi jam’iyyar APC da gazawa a Najeriya, inda ya ƙara da cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da Shugaba Tinubu sun kasa cika alƙawuran da suka ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe.
Amma da yake mayar da martani, Felix Morka ya bayar da hujjar cewa Shugaba Tinubu na ɗaukar matakai masu tsauri domin sake farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan wanda ya daɗe a durƙushe.
Me APC ta ce kan gwamnatin Tinubu?
Kakakin na APC ya yi bayanin cewa sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya kawo sun kawo halin ƙunci a ƙasar nan, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
"Gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu tana ɗaukar kwararan matakai domin sake farfaɗo da tattalin arzikin ƙasarmu da ya daɗe da durƙushewa, inganta tsaron ƙasa da dawo da ƙasar nan kan hanyar samun ci gaba mai ɗorewa."
"Ba shakka, waɗannan sauye-sauyen sun ƙarawa al’ummarmu wahalhalu. Hasalima gazawar gwamnatocin baya na kawo waɗannan sauye-sauyen da magance matsalar, shi ne dalilin da ya sanya tattalin arziƙin ƙasar nan ya daɗe a durƙushe."
- Felix Morka
Tinubu ya magantu kan cire tallafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ta cire tallafin man fetur ne saboda a samu isassun kuɗaden shiga da za a yi wa ƴan Najeriya aiki.
Shugaba Tinubu ya ce ba domin ƙuntatawa mutane ya ɗauki wasu matakai ba, ya yi haka ne domin ceto tattalin arzikin ƙasar nan wanda ya fara tangal-tangal.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng