Ambaliya: Jami'an Agaji Sun Maƙale a Ruwa daga Zuwa Ceton Mutane a Arewa
- Jami'an hukumar ba da agajin gaggawa ta Borno SEMA sun maƙale a wani yanki da suka je kai kayan agaji da ceto mutane
- Shugaban SEMA, Barkindo Mohammed na cikin tawagar jami'an da suka maƙale bayan kai wa mutane ɗauki a yankin Gozari
- An tattaro cewa dubban mutane sun rasa gidajensu, wasu ba su san wurin da za su dosa ba sakamakon ambaliya a Maiduguri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno - Darakta janar na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Borno (SEMA) Barkindo Mohammed da tawagarsa sun maƙale daga zuwa ceto mutane a Maiduguri.
Idan ba ku manta ba ruwan dam din Alau ya yi ambaliya da safiyar ranar Talata, 10 ga watan Satumba, inda ya kwarara zuwa Unguwanni da garuruwa a Borno.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ambaliyar ruwan ta mamaye gidajen dubannin mutane tare da lalata kadarori a babban birnin jihar da wasu sassa.
Borno: Jami'an SEMA sun fara aikin ceto
A ƙoƙarin ceto waɗanda ambaliyar ruwan da rutsa da su ne wasu jami'an NEMA suka maƙale a yankin da ruwan ya mamaye.
Da yake hira da hukumar dillancin labarai (NAN), Barkindo Mohammed ya tabbatar da cewa tuni jami'an hukumar SEMA suka duƙufa aikin ceto da kaiwa mutane jakunkunan ruwa.
"Yanzu ba daɗewa muka je kai ɗauki domin ceto wasu bayin Allah, daga nan muka wuce zuwa Gozari domin rabawa mutane jakunkunan ruwa.
"Maganar da nake yi da ku yanzu haka ni kai na na maƙale, mun zo domin ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su, kuma mun maƙale ni da jami'aina."
Wane hali mutane ke ciki a Borno?
A halin yanzu, daruruwan mutane suna kan tituna ba tare da sanin inda za su samu mafaka ba.
Rahoto ya nuna wasu kuma na kwance ko zaune a karkashin inuwar bishiya tare da iyalansu suna jiran tsammani.
An kawo dabarun magance ambaliya
A wani rahoton kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce ta shirya wasu sababbin tsare tsare da za su taimaka wajen magance matsalolin ambaliyar ruwa a Najeriya.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci Maiduguri da ambaliya ta yiwa mummunar barna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng