"Abu 1 Muke Jira," Gwamna Ya Faɗi Abin da Ya Hana Shi Fara Biyan Albashin N70,000

"Abu 1 Muke Jira," Gwamna Ya Faɗi Abin da Ya Hana Shi Fara Biyan Albashin N70,000

  • Gwamnan jihar Delta ya yiwa ma'aikata albishirin cewa gwamnatinsa ta shirya aiwatar da dokar sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000
  • Sheriff Oborevwori ya ce a yanzu yana jiran tsarin da za a bi wajen aiwatar da dokar ƙarin albashin shiyasa bai fara biyan ma'aikata ba
  • Ya faɗi haka ne a wurin taron da aka shirya domin karrama magatakardar majalisar dokokin jihar Delta bayan ta yi ritaya daga aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta, a ranar Talata, ya ce gwamnatinsa na jiran taswirar sabon mafi karancin albashi na N70,000.

Gwamnan ya ce taswirar kaɗai ta dakatar da shi daga fara biyan ma'aikata N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Kara karanta wannan

Sakataren gwamnatin jiha ya yi murabus, gwamna ya naɗa mace nan take

Gwamna Sheriff Oborevwori.
Gwamnan Delta ya shirya fara biyan sabon mafi mafi ƙarancin albashi na N70,000 Hoto: Rt. Hon. Sheriff Oborevwori
Asali: Facebook

Oborevwori ya faɗi haka ne a wurin liyafar da aka shirya domin karrama magatakardar majalisar dokokin Delta bayan ta yi ritaya, rahoton Vanguard.

Misis Lyna Ocholo ta yi ritaya daga matsayin magatakardar majalisa kuma Gwamna Oborevwori ya naɗa ta a matsayin babbar sakatariyarsa.

Gwamnan Delta ya yi magana kan albashi

Da yake jawabi a wurin taron a zauren majalusar dokokin, gwamnan Delta ya ce yana jiran taswirar biyan albashin domin gudun tafka kuskure.

“Muna jiran jadawalin tsarin da za a bi wajen aiwatar da sabon mafi karancin albashi saboda ba mu son yin kuskure," in ji gwamnan.

Ya taya Misis Ocholor murna bisa nasarar kammala aikin gwamnati, ya kuma gode wa ma’aikatan majalisar bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin yana kakakin majalisa.

Gwamna ya godewa ƴan majalisa

Kara karanta wannan

APC ta faɗi gwamnan da take zargin yana shirya gagarumar zanga zanga a Najeriya

Gwamna Sheriff Oborevwori ya ƙara da cewa ma'aikata ba su taɓa shiga yajin aiki ba a lokacin da yake shugaban majalisar dokoki ta bakwai da takwas.

Ya godewa shugaban majalisar dokokin jihar Delta na yanzu da sauran mambobi bisa yadda suke ba gwamnati haɗin kai tare da yin aiki tare, Tribune ta rahoto.

Gwamna Dikko ya shirya biyan N70,000

A wani rahoton kuma gwamnatin jihar Katsina ta sanar da shirin fara biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashi na N70,000 da aka cimma matsaya da NLC.

Dikko Umaru Radda ne ya sanar da haka kuma ya ce jihar Katsina za ta kasance a gaba gaba kan maganar ƙarin albashin ma'aikata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262