Borno: Muhimman Wurare 5 da Ambaliyar Ruwa Ta Fi Yin Barna a Maiduguri
Mazauna jihar Borno sun shiga mawuyacin hali yayin da aka rika neman mafaka bayan ambaliya ya mamaye unguwanni da matsugunan jama'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno - Shugabar hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa, Zubaida Umar ta ce a wuraren da ambaliya ta lalata akwai yankin Shehuri, Gambomi da Budum
A sakon da ta wallafa a shafinta na X, ta ce sauran wuraren sun hada da Bulabulin, Adamkolo, Millionaires Quarters, Kasuwar Litinin da Gwange.
Legit ta tattaro wasu daga cikin wuraren da ambaliyar ta lalata, yayin da mazauna jihar su ka ce ruwan ya fara janye wa.
1. Ruwa ya mamaye fadar Shehun Borno
Ambaliyar ruwa ta mamaye fadar Shehun Borno. Muhammad Idris, mazaunin Maiduguri ne inda lamarin ya yi kamari, ya ce akwai hanyar ruwa a bayan fadar Sarkin.
Ya shaida wa Legit cewa ruwan ya fashe ta madatsun ruwan Gadabul da Alau, wanda hakan ne ya ta'azzara lamarin a hanyarsa ta bayan fadar Shehun.
2. Ambaliya ta lalata makabartu
Ambaliyar da aka shafe shekaru ba a ga irinta ba ta lalata makabartu, yayin da ruwa mai karfi ya rika bude kaburbura.
Masana a bangaren lafiya sun ce akwai bukatar a gaggauta daukar matakan gaggawa domin dakile yaduwar cutuka da lamarin zai iya jawo wa.
3. Ruwa ya balle gidan adana namun dawa
Mahukunta a jihar Borno sun gargadi mazauna Maiduguri su bi a hankali bayan ambaliya ta wanke namun dawa da aka adana a gidan adana dabbobi.
Ana fargabar dabbobin za su iya illata mazauna jihar yayin da kowa ke neman inda zai fake saboda ambaliyar.
4. Ambaliya ta lalata gidan gyaran hali
Ambaliyar da aka yi a Maiduguri ya lalata wasu bangarorin kurkuku da ke Maiduguri, lamarin da ya ba daurarru damar guduwa.
Tuni hukumomi su ka ce an shiga farautar dararrun saboda mafi akasarinsu barazana ne ga al'umma.
5. Ambaliya: An rufe jami'ar UNIMAID
Daliban jami'ar Maiduguri (UNIMAID) sun tafi hutun dole kuma na sai baba ta gani bayan ambaliya ta jawo cikas.
Mahukuntan jami'ar sun mika jajensu ga dalibai da malaman da lamarin ya rutsa da su, inda aka ce an dauki matakin ne domin ci gaba da kare su.
Gwamnatin Tinubu za ta kai agajin ambaliya
A baya mun wallafa cewa gwamnatin tarayya ta mika sakon jaje ga gwamnatin jihar Borno bayan ambaliyar ruwa ta yi kokarin cinye Maiduguri, yayin da jama'a ke neman mafaka.
A sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce gwamnati a shirye ta ke ta taimakawa gwamna Babagana Zulum kan lamarin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng