Ma'aikata Sun Shiga Yajin Aiki: Najeriya Na Iya Fuskantar Tangardar Sadarwa

Ma'aikata Sun Shiga Yajin Aiki: Najeriya Na Iya Fuskantar Tangardar Sadarwa

  • Ma'aikata a bangaren sadarwa karkashin kungiyar manyan ma’aikata a harkar (PTECSSAN) sun tsunduma yajin aiki a fadin kasar
  • An rahoto cewa wannan yajin aikin zai zama barazana ga ayyuka da kuma yiwuwar katse hanyoyin sadarwa ga miliyoyin mutane
  • Sakataren kungiyar, Okonu Abdullahi ya ce an umarci dukkanin 'ya'yan kungiyar da ka da su mayar da martani ga katsewar sadarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bangaren sadarwa a Najeriya na dab da fuskantar cikas yayin da kusan ma’aikata 800 daga kungiyar manyan ma’aikatan sadarwa (PTECSSAN) suka shiga yajin aikin.

Wannan matakin zai zama barazana ga ayyuka a duk faɗin ƙasar, da kuma yiwuwar katsewar hanyoyin sadarwa ga miliyoyin mutane.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun mamaye ofishin SERAP awanni bayan kungiyar ta nemi a binciki NNPCL

Ma'aikata a bangaren sadarwa sun shiga yajin aiki a fadin Najeriya
Najeriya na fuskantar barazanar tangardar sadarwa bayan ma'aikata sun shiga yajin aiki. Hoto: Darren McCollester, Tim Robberts
Asali: Getty Images

Yajin aikin da aka fara tun ranar Litinin, ya kunshi ma’aikatan kwangila da ke karkashin kungiyar ta PTECSSAN inji rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yajin aikin ma'aikatan sadarwa

Bukatun kungiyar sun hada da maido da ma’aikatan da aka kora, amincewa da kungiyar a hukumance, inganta yanayin aiki, da kuma biyan hakkokin 'yan kungiyar.

Kungiyar ta bayyana yajin aikin a matsayin "abin da ba za a iya kaucewa ba" saboda mummunan yanayin wurin aiki da kuma kin amincewa da ‘yancinsu na kafa kungiya.

Sakataren kungiyar, Okonu Abdullahi ya ce su ne ke gudanar da muhimman ayyuka a bangaren sadarwa, ciki har da kula manyan kamfanonin sadarwa irin su IHS da Huawei.

“Tasirin wannan yajin aikin na da yawa sosai, domin mun umurci 'yan kungiyarmu da kada su mayar da martani ga katsewar sadarwa."

- A cewar Okonu.

Kara karanta wannan

Dattawan Yarabawa sun yi adawa da karin kudin fetur, sun aika sako ga Tinubu

Kamfanonin da yajin-aikin ya shafa

'Yan ƙungiyar sun haɗa da injiniyoyin kula da na'urori, injiniyoyin kula da watsa ayyuka, injiniyoyin ayyukan abokin ciniki, da injiniyoyin fasahar sadarwa ta 'fiber'.

Jaridar The Punch ta rahoto kamfanonin da yajin aikin ya shafa sun hada da Huawei Technologies Nigeria, Tylium Nigeria Limited, Specific Tools & Techniques.

Sauran sun hada da CPNL (Chinese Pacific Networks Limited), CITCC (China International Telecommunications Construction Corporation), da JUSPARTNER.

Tangardar sadarwa lokacin zanga zanga

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ce ko kusa ba ta da hannu a tangardar sadarwa da aka samu yayin da matasa ke gudanar da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin zamani, Bosun Tijani ya ce ofishinsa bai bayar da umarnin kawo tangarda a layukan sadarwa a lokacin zanga zangar ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.