Bayan Ruwa Ya Mamaye Borno, Daurarru Sun Samu Hanyar Tserewa daga Kurkuku

Bayan Ruwa Ya Mamaye Borno, Daurarru Sun Samu Hanyar Tserewa daga Kurkuku

  • Mamakon ruwan sama a Borno ya dagula lamura, inda da yawa daga cikin mazauna jihar su ka rasa matsugunansu
  • Daurarru da aka ajiye a kurkuku a jihar na daga cikin wadanda su ka rasa wurin zama, lamarin ya ya ba su damar tserewa
  • Zuwa yanzu, an tabbatar da daurarru da yawa sun gudu, sai dai ba a kai ga sanin adadin wadanda su ka tsere ba zuwa yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Daurarrun da ba a kai ga sanin adadinsu ba sun samu damar tserewa daga kurkukun da aka ajiye su saboda wau dalilai a Borno.

Kara karanta wannan

"Za mu kai dauki Maiduguri": Tinubu ya aika sako ga Zulum bayan ambaliyar ruwa

Mamakon ruwan sama da ballewar madatsar ruwa ya jawo ambaliya da ya mamaye jihar,wanda ya ba daurarrun damar tserewa cikin sauki.

Borno
Daurarru sun tsere Bayan ambaliya a Borno Hoto: Belyameen Ahmad Magami
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa halin da gidajen kurkukun ke ciki bayan ambaliyar ne ya ba daurarrun damar guduwa, sai dai ba duka ne su ka tsere ba.

Borno: Ana fargabar daurarru na da makamai

Mahukunta a Borno sun tabbatar da guduwar wasu daga cikin daurarrun da ke kurkuku a jihar sakamakon ambaliyar ruwa bayan ballewar madatsar ruwa.

Mahukuntan sun ce ana fargabar wasu daga cikin wadanda su ka gudu na dauke da makamai kuma za su iya zama barazana ga zaman lafiya a jihar.

An shiga neman daurarru a jihar Borno

Yanzu haka jami'ai da sauran masu ruwa da tsaki sun fantsama neman daurarrun da su ka gudu daga gidajen ajiya da gyaran hali a Borno.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Borno ke fuskantar ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru 30

An samu rahoton cewa ana kokarin gano wadanda su ka gudu tare da sake kama su domin mayar da su gidan daurarrun bayan an nemi gudunmawar karin jami'an tsaro.

Ambaliya: Shettima zai ziyarci Borno

A baya mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana damuwarsa kan ambaliyar ruwa da ta mamaye mafi akasarin jihar Borno, jihar mataimakinsa.

A zantawarsa da manema labari, mataimakin shugaban kasar, Sanata Kashim Shettima ya ce shugaba Tinubu ya umarce shi ya gaggauta zuwa jihar domin ganin halin da ake ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.