Tinubu Ya Kadu da Ambaliyar Ruwa a Maiduguri, Ya Ba Shettima sabon Umarni
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya umurci mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da ya gaggauta barin birnin tarayya Abuja zuwa Maidugurin jihar Borno.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
An rahoto cewa Tinubu ya ba Shettima wannan umarnin ne biyo bayan ambaliyar ruwa da ta barke a Maiduguri sakamakon ballewar madatsar ruwa ta Alau.
Shettima zai tafi Maiduguri
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Kashim Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja, a wajen taron shekara-shekara na Banki da Kudi (CIBN) karo na 17.
“Bayan wannan taron, da amincewar shugaban kasa zan garzaya Maiduguri. Ambaliyar ruwa ta mamaye birnin gaba daya.
Ambaliyar ruwan ba ta keɓanta ga wani yanki na ƙasar kadai ba. Muna fuskantar wannan matsalar a Bayelsa da Sokoto.
"Ku sani cewa shugaban kasa yana da kwana da tashi da al'ummar kasar a zuciyarsa kuma zai yi duk abin da ya kamata domin tafiyar da al'amura."
Gwamnati ta jajantawa 'yan Borno
Shettima ya bayyana juyayin gwamnatin Shugaba Tinubu ga duk wadanda iftila'in ambaliyar ruwa ya shafa a fadin kasar nan.
"Ina so in yi amfani da wannan dama domin jajanta wa jama'ar kasarmu da iftila'in ambaliyar ruwa ya shafa a sassan kasar."
- A cewar Shettima.
Maiduguri: Madatsar Alau ta balle
A wani labarin, mun ruwaito cewa, mazauna Maiduguri da dama sun rasa matsugunansu bayan ambaliyar ruwa da ta barke sakamakon ballewar madatsar ruwa ta Alau.
Gwamnatin Borno ta bukaci mazauna Maiduguri musamman wadanda ke kusa da kogi da su gaggauta daukar matakan kare kansu daga ambaliyar ruwan.
Asali: Legit.ng