Dalilin da Ya Sa Borno ke Fuskantar Ambaliyar Ruwa Mafi Muni cikin Shekaru 30

Dalilin da Ya Sa Borno ke Fuskantar Ambaliyar Ruwa Mafi Muni cikin Shekaru 30

  • A shekarar 1994 ne madatsar ruwa ta Alau ta balle wanda ya haddasa ambaliyar da ta shafe kusan rabin Maiduguri, abin da ba a taba gani ba
  • A ranar 10 ga Satumbar 2024, gwamnatin ta aika sako ga mazauna Maiduguri musamman kusa da kogi da su dauki matakan kare kansus
  • A cikin shekaru 30, jihar Borno ta yi fama da ambaliyar ruwa, wanda ya jawo asarar rayuka, lalacewar amfanin gona da gidajen jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Gwamnatin jihar Borno ta yi zargin cewa mamakon ruwan sama da aka shafe mako ana yi tare da cika da batsewar madatsar ruwa ta Alau ne ya jawo ambaliya a Maiduguri.

Kara karanta wannan

"Za mu kai dauki Maiduguri": Tinubu ya aika sako ga Zulum bayan ambaliyar ruwa

Gwamnatin ta ce madatsar ruwa ta Alau ta fashe bayan ta yi cikar da ya wuce kima, wanda ya jawo ambaliyar da ta mamaye dubunnan gidaje a babban birnin jihar.

Ambaliyar ruwa ta barke a Borno bayan ballewar madatsar ruwa ta Alau
Borno: Gwamnati ta nemi mazauna Maiduguri da su dauki matakan kare kansu bayan ambaliya. Hoto: Justin Sullivan
Asali: Getty Images

Tasirin ambaliyar ruwa a Borno

Lokacin karshe da madatsar Alau ta samu irin wannan matsala shi ne a shekarar 1994, inji rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce fashewar matsalar ruwan a 1994 ya haifar da ambaliyar da ba a taba ganin irinta ba a Maiduguri inda ruwan ya mamaye kusan rabin garin.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da tsaro Borno, Farfesa Usman Tar ya fitar a safiyar Talata, ya yi kira da mazauna kusa da madatsar su gaggauta barin yankin.

Gwamnatin Borno ta aika sako

Daily Post ta rahoto sanarwar Farfesa Usman ta ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan

Tinubu ya kadu da ambaliyar ruwa a Maiduguri, ya ba Shettima sabon umarni

"Saboda yawan ruwan da ba a saba gani ba a bana, muna kira ga daukacin mazauna bakin kogi da su dauki matakin kare kansu da dukiyoyinsu cikin gaggawa.
"Madatsar ruwa ta Alau ta fashe a halin yanzu kuma ruwan da fitowa ya fara lalata gonaki tare da tunkarar kogin yankin."

Farfesa Usman ya kuma bukaci mazauna yankunan da abin ya shafa da su bi hanyoyin da aka ware na fita daga yankin domin tsira da rayukansu cikin aminci.

Ambaliya ta mamaye fadar Shehun Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa ambaliyar ruwa da ta barke a Maiduguri ta mamaye gidan mai martaba Shehun Borno, Alhaji Garba El-Kanemi a ranar Talata.

An rahoto cewa ambaliyar da ta faru bayan ballewar madatsar ruwa ta Alau sakamakon mamakon ruwan sama ta tilasta basaraken neman mafaka a gidan gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.