An yi Yamutsi bayan Soja Ya Harbe Mutum a Arewa, Matasa Sun yi Fashe Fashe

An yi Yamutsi bayan Soja Ya Harbe Mutum a Arewa, Matasa Sun yi Fashe Fashe

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Benue na nuni da cewa an samu yamutsi bayan an zargi wani sojan Najeriya da harbe wani mutum
  • An ruwaito cewa matasa sun nuna bacin rai yayin da suka so tayar da rikici bayan an dauki gawar mutumin da sojan ya bindige har lahira
  • Bayan kisan, rundunar yan sanda ta kama sojan da ake zargi domin yin bincike da tabbatar da adalci ga wanda aka kashe cikin mota

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Rundunar yan sanda ta kama wani soja bayan an zarge shi da harbe wani mutum har lahira a jihar Benue.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun koma bautar da mutane a gonaki Arewacin Najeriya

An ruwaito cewa ana zargin sojan da harbin matashin ne yayin da yake tafiya a cikin motarsa.

Benue
Yan sanda sun kama soja a Benue. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Tribune ta wallafa cewa wasu matasa sun yi nufin tayar da yamutsi a yankin da abin ya faru.

Yadda soja ya harbe matashi har lahira

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa sojan da ake zargi da kisan ya harbi mutumin ne yayin da yake tafiya a cikin mota.

Sun bayyana cewa yayin da sojan ya harbi motar a baya sai ta karkata ta nufi wata gona daga nan kuma sai mutumin ya fadi a kan sirdi ya mutu.

Yan sanda sun kama soja kan kisan kai

Rundunar yan sanda a jihar Benue ta tabbatar da kama sojan da ake zargi da kisan mai suna Aboy Bonny.

Shugaban yan sanda a yankin, Edmund Afraimu ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a wani kamfanin Dangote na siminti.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta barke kan karin kuɗin fetur, an rufe gidajen mai da shaguna

Matasa sun tayar da yamutsi a Benue

An ruwaito cewa wasu matasa a wajen da abin ya faru sun dauki gawar wanda aka kashe suna zanga zanga har kamfanin simintin Dangote inda ake hasashen mutumin yana aiki.

Daily Post ta wallafa cewa matasan sun yi fashe fashen motoci da toshe hanya inda da kyar shugaban karamar hukumar Gboko ya shawo kan lamarin.

Gwamna zai mallakawa mutane bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya nuna takaici kan yadda yan bindiga ke kashe mutane da sace su a Arewacin Najeriya.

Dikko Umaru Radda ya ce a shirye yake ya ba mutane bindigogi domin su rika fafatawa da yan ta'adda masu garkuwa da mutane a Katsina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng