Maiduguri: Ambaliya Ta Mamaye Gidan Sarki, Shehun Borno Ya Nemi Mafaka

Maiduguri: Ambaliya Ta Mamaye Gidan Sarki, Shehun Borno Ya Nemi Mafaka

  • A yau aka wayi gari da mummunar ambaliyar ruwa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda mutane da dama suka rasa gidaje
  • Ruwa ya shiga gidaje da dama da kasuwanni inda ya jawo asarar dukiya mai dimbin yawa ga mazauna birnin Maiduguri
  • Legit ta tattauna da wata yar jihar Borno, Fatima Jidda domin jin halin da suka shiga a lokacin ambaliyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Rahotanni da suka fito daga jihar Borno na nuni da yadda ake tafka asara sakamakon ambaliyar ruwa.

An ruwaito cewa ambaliyar ruwa ta mamaye wurare da dama ciki har da gidan mai martaba Shehun Borno.

Kara karanta wannan

Borno: Ambaliya ta kashe yan Boko Haram sama da 100 a Sambisa

Ambaliyar ruwa
Ruwa ya malala gidan Shehun Borno sakamakon ambaliya. Hoto: Bulama Adamu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa mutane da dama sun ce ba su taba ganin ambaliyar ruwa kamar na wannan lokacin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ambaliya ta mamaye gidan Shehun Borno

Rahotanni na nuni da cewa ruwa ya mamaye gidan Shehun Borno bayan wasu wurare da dama a Maiduguri.

Wasu mazauna birnin Maiduguri sun bayyana cewa mai martaba Shehun Borno, Alhaji Garba El-Kanemi ya nemi makafa a gidan gwamnatin jihar.

An yi gardadin ambaliya a jihar Borno

Wani wanda abin ya shafa, Usman Babagana ya bayyana cewa dama an musu gargaɗi kan yiwuwar ambaliyar ruwan.

Sai dai Usman Babagana ya ce ba su yi tsammanin abin zai zo da muni haka ba kuma ba su da inda za su gudu shi yasa ba su canza waje ba.

Wuraren da aka yi ambaliya a Borno

Kara karanta wannan

Borno: Mutanen Maiduguri sun wayi gari da labari mai daɗi bayan ambaliyar da ta afku

Daily Trust ta wallafa cewa Gwange, Post Office Modugari na cikin wuraren da ambaliyar ta shafa sosai.

Mazauna birnin Maiduguri sun yi fatan cewa Allah yasa ambaliyar ba za ta jefa su cikin mummunan hali ba bayan yanayin da ake ciki.

Legit ta tattauna da yar jihar Borno

Wata yar jihar Borno, Fatima Jidda ta zantawa Legit cewa da kyar ta kubuta kasancewar ruwan ya kai har wuyanta.

Fatima Jidda ta bayyana cewa ruwan ya zo da karfi yana kara inda ya rika kayar da mutane suna mutuwa a cikinsa.

Ambaliya ta yi barna a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa mutane 1,664 ne suka rasa gidajensu a wasu yankunan jihar Sokoto sakamakon mamakon ruwan saman da aka tafka.

An ruwaito cewa ruwan saman ya wawushe gonakin jama'a a wasu kauyukan Dantudu, Balakozo, Gidan Tudu da Tsitse Towns, da sauransu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng