Ambaliyar ruwa: Gwamnatin Borno za ta rushe gidaje 1,300
- Gwamnatin Jihar Borno za ta rushe wasu gidaje kimanin 1,300 da ke kan hanyoyin ruwa da gaɓar tafi a Maiduguri
- Gwamnati Jihar ta dauki wannan matakin ne domin kiyaye kazantar ambaliyar ruwa a birnin saboda gine-gine sun rufe hanyoyin ruwa
- Gwamnatin ta kuma gargadi al'umma su guji yin gini a wuraren da ba su dace ba domin gwamanti na iya rusa ginin ba tare da an biya su wani haki ba
Gwamnatin Jihar Borno a ranar Laraba ta ce ta ware wasu gidaje 1,300 da za ta rushe saboda an gina su a kan hanyoyin ruwa da gaɓar rafi a Maiduguri, babban birnin jihar.
Ambaliyar ruwa ta shafi wasu ɓangarori na jihar cikin watanni biyu da suka gabata kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Da ya ke magana yayin taron manema labarai a ranar Laraba a Maiduguri, Sakataren Hukumar Kula da Bayanan Yanayi, Adam Bababe ya ce dole a dauki matakin gaggawa kuma za a rushe gine-ginen da aka yi a wuraren da ba su dace ba.
DUBA WANNAN: Yadda tsohon minista ya 'zazzagi' dan jarida saboda ya masa wata tambaya
Ya ce, "Wannan ba bita da ƙulli bane ko lamari na addini. Mun tattauna da shugabannin kungiyar Kiristoci ta CAN a Borno kuma sun fahimci cewa ya zama dole a ɗauki matakin ne domin kare wasu gidaje daga ambaliyar ruwa.
"An gine kimanin gidaje 1,300 a kan hanyoyin ruwa kuma an ware su domin a rushe su. Idan bamu rushe gidajen ruwa ya samu hanya ba, gidaje da dama a birnin za su yi ambaliya."
Ya yi kira ga mazauna jihar su dena gina gidaje a wuraren da ba su dace ba musamman a hanyoyin ruwa da gaɓar ruwa.
Kazalika, ya gargadi masu gine-gine a kan filayen da ba bisa ka'ida suka same su ba cewa gwamnati na iya rushe su ba tare da biyan su wani abu ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng