"Akwai Matsala": Gwamna Ya Ba Makarantu Hutu saboda Gudun Rasa Rayukan Ɗalibai

"Akwai Matsala": Gwamna Ya Ba Makarantu Hutu saboda Gudun Rasa Rayukan Ɗalibai

  • Gwamnatin Borno ta ba makarantun sakandire da firamare hutun kwanaki 14 domin kaucewa yiwuwar rasa rayuka sakamakon ambaliya
  • Kwamishinan ilimin kimiyya da fasaha na jihar, Lawal Wakilbe ya ce an ɗauki wannan mataki bayan tattaunawa da kwamitin ambaliya
  • Maiduguri, Jere da wasu ƙananan hukumomin Borno na cikin yankunan da ake ƙara samun ambaliya a jihar a ƴan kwanakin nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Gwamnan Borno da ke Arewa maso Gabas, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ba da umarnin rufe dukkan makarantun jihar nan take.

Gwamna Zulum ya ɗauki wannan matakin ne domin gujewa rasa rayuka sakamakon ambaliyar ruwan da ke faruwa a Maiduguri, babban birnin Borno.

Kara karanta wannan

Zaɓen Kano ya gamu da cikas, Majalisar dokoki ta ɗauki mataki kan ciyamomi 44

Gwamna Zulum.
Gwamna Zulum ya rufe makarantu don gudun rasa rayuka a ambaliyar Borno Hoto: @GovZulum
Asali: Facebook

Kwamishinan Ilimin Kimiyya da Fasaha jihar, Injiniya Lawal Wakilbe ya tabbatar da hakan a wata zantawa da wakilin Daily Trust ta wayar tarho a ranar Litinin.

Gwamna Zulum ya bada hutun mako 2

Lawal Wakilbe ya ce Gwamna Zulum ya umurci dukkan makarantun firamare da sakandare da su rufe, su tafi hutun makonni biyu gabannin ambaliya ta janye.

Ya ce wannan matakin na bada hutun makarantu ya zama dole bayan tattaunawa da kwamitin ambaliyar ruwa domin kare rayukan al'umma.

Mafi akasarin kauyukan dukkan kananan hukumomin jihar Borno na fama da ibtila'in ambaliyar ruwa musamman Maiduguri, Jere da wasu yankuna.

Gwamnatin Borno ta kafa kwamitin ambaliya

Tun farko dai gwamnatin Borno ta kafa kwamiti na musammna da zai yi kokarin lalubo hanyoyin magance ambaliya da kuma kai agaji ga waɗanda ta rutsa da su.

Kara karanta wannan

Miyetti Allah ta gargadi makiyaya, an dauki wasu matakan kashe wutar rikici

Sakataren gwamnatin jihar, Bukar Tijjani, shi ne shugaban kwamitin, wanda a yanzu ya ba da shawarar a ba ɗaliban makarantu hutu don gujewa rasa rai.

Kwamishinan ilimi, Wakilbe ya ce ana sa ran wannan matakin zai taimaka wajen kare mutane daga ibtila'in ambaliya, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Gwamna Sulodo ya musanta korar hadimi

Kuna da labarin gwamnan jihar Anambra ya musanta raɗe-raɗin tsige hadiminsa kan bidiyon da aka saki na gwamna yana rawa a soshiyal midiya.

Farfesa Charles Soludo ya bayyana jita-jitar a matsayin ƙarya mara tushe, inda ya tabbatar da cewa babu wanda ya kora daga aiki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262