"Ana Cin Zarafin 'Dan Adam," Amnesty Int'l, Shehu Sani Sun Yi Tir da Kutsen DSS a Ofishin SERAP
- Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana rashin dacewar kutsen da jami'an DSS su ka yi wa ofishin SERAP
- Ita ma kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty Int'l ta ce akwai fargabar Bola Tinubu ya na kokarin dakile kungiyoyin kwatar yanci
- A safiyar Litinin ne jami'an tsaron da ake tsammanin na DSS ne su ka kusta ofishin kungiyar SERAP mai kare hakkin al’ummar kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bayyana cewa matakin da jami'an DSS su ka dauka na kutse ofishin SERAP bai dace ba.
A safiyar Litinin din nan ne kungiyar kare hakkin al'umma da tattalin arzikin kasa (SERAP) ta bayyana cewa wasu jami'an hukumar tsaro ta fararen kaya sun kutsa ofishinsu.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Shehu Sani ya nemi gwamnatin tarayya ta mutunta dokar da ta kare yan kasa da masu fafutukar kare yancinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amnesty ta yi tir da kutsen jami'an DSS
Ita ma hukumar kare hakkin dan Adam ta Amnesty Int'l ta bayyana cewa kutsen jami'an DSS a ofishin SERAP haramtacce ne.
Punch ta wallafa cewa matakan da gwamnatin Bola Tinubu ke dauka na dakile masu adawa da ita sun yi tsauri.
An nemi hana DSS cin zarafin jama'a
Sanata Shehu Sani ya nemi gwamnatin tarayya ta daina amfani da ikonta wajen cin zarafin kungiyoyi da ke fafutuka a kasar nan.
Ita ma kungiyar Amnesty Int'l ta ce dole ne hukumomin tsaro su rika karewa tare da mutunta darajar yan adam kamar yadda doka ta tanada.
DSS ta kutsa ofishin SERAP
A baya mun wallafa cewa kungiyar kare hakkin al'umma da tattalin arzikin kasa (SERAP) ta koka kan yadda ta ce jami'an hukumar tsaro ta DSS sun ziyarci ofishinta.
A sanarwar da kungiyar ta fitar, ta ce jami'an DSS sun nemi ganawa da daraktanta bayan an mamaye ofishin ba bisa ka'ida ba, inda ta nemi shugaban kasa ya takawa DSS birki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng