Miyetti Allah Ta Gargadi Makiyaya, An Dauki Wasu Matakan Kashe Wutar Rikici

Miyetti Allah Ta Gargadi Makiyaya, An Dauki Wasu Matakan Kashe Wutar Rikici

  • Kungiyar makiyaya ta MACBAN ta dauki matakin inganta dangantaka tsakaninsu da manoma a yunkurin magance rikici
  • An haramtawa yara masu karancin shekaru kiwo a jihar Kwara, tare da haramta kiwon dare domin inganta dangantakar
  • Shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa, Alhaji Baba Othman Ngelzarma ya bayyana muhimmancin wannan alaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kwara - Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association (MACBAN), ta bayyana matakin da ta dauka wajen rage rikicin manoma da makiyaya.

Kungiyar MACBAN ta haramtawa yara masu karancin shekaru kiwon dare a fadin jihar Kwara a yunkurin rage rigingimu tsakanin manoman da masu kiwo.

Kara karanta wannan

2027: Tafiyar Shekarau na kara ƙarfi da Namadi Sambo da Ministan Buhari suka goyi baya

Shanu
MACBAN ta haramta kiwon dare Hoto: LUIS TATO
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban MACBAN na kasa, Alhaji Baba Othman Ngelzarma ne ya bayyana haka yayin kaddamar da shugabancin kungiyar na jihar Kwara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran matakan da Miyetti Allah ta dauka

Kungiyar MACBAN ta dauki matakin haramta kiwon dare a fadin jihar Kwara domin rage matsalolin da ke jawo rigingimu tsakaninsu da manoma.

Shugaban kungiyar, Alhajai Ngelzarma ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa kiwon dare wata hanya ce ta takalar tsokana da neman rigima da gangan.

Dalilin daukar matakan da Miyetti Allah ta yi

Kungiyar makakiyan kasar ta ce ta dauki matakan haramta kiwon dare da barin kananan yara su rika kiwo saboda magance rikicin manoma da makiyaya.

Kungiyar ta bayyana cewa dangantaka mai kyau tsakanin manoma da makiyaya abu ne mai muhimmancin gaske, inda ta bukaci shugabannin kungiyar su tabbata an bi dokokin.

Kara karanta wannan

Bayan tura sojoji Sakkwato, 'yan Arewa sun fara shinshino karshen rashin tsaro

Miyetti Allah ta koka kan batan makiyaya

A baya mun ruwaito cewa kungiyar makiyaya ta MACBAN ta koka kan batan makiyaya akalla 11 da shanunsu akalla 33 a jihar Anambra.

A sanarwar da mataimakin daraktan MACBAN, Gidado Siddiqi ya fitar, ya bayyana cewa 'ya'yan kungiyar na kiwonsu a bi sa doka ba kamar yadda ake danganta su da ta'addanci ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.