Bayanai Sun Fito kan Dalilin Kama Shugaban Kwadago da DSS Ta yi
- Rahotanni da suka fito daga wasu jami'an tsaro sun nuna an kama shugaban kwadago ne bisa zargin kin amsa gayyatar 'yan sanda
- Ana hasashen cewa wani kamfanin jigilar jiragen sama ne ya kai Joe Ajaero kara wajen 'yan sandan Najeriya kan wasu abubuwa
- A yau Litinin ne jami'an DSS suka kama Joe Ajaero yayin da yake kokarin tafiya Birtaniya domin halartar wani taron 'yan kwadago
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bayanai sun fara fitowa kan dalilin kama shugaban kwadago da hukumar DSS ta yi a Abuja.
An samu rahotanni kan cewa shugaban kwadago bai amsa wata gayyata da hukumar DSS ta yi masa ba ne.
Jaridar the Cable ta wallafa cewa wasu jami'an tsaro sun ce kamfanin jigilar jiragen sama na Air Peace ne ya kai Joe Ajaero kara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NLC ta yi gargadi bayan kama Ajaero
Bayan kama Joe Ajaero a safiyar yau, kungiyar kwadago ta bukaci yan kungiyarta su zauna kan shirin ko-ta-kwana.
Legit ta ruwaito cewa yan kwadago sun bukaci a gaggauta sakin Joe Ajaero inda suka ce kama shi ba ya kan ƙa'ida.
Dalilin kama shugaban kwadago
Rahotanni sun nuna cewa kamfanin jigilar jiragen sama na Air Peace ne ya shigar da Joe Ajaero kara wajen yan sanda.
Bayan yan sanda sun gayyaci Joe Ajaero domin amsa tambayoyi shi kuma ya yi biris da gayyatar da aka masa kamar yadda majiyar jami'an tsaro ta tabbatar.
Bayan haka, an ruwaito cewa jami'an DSS ma sun gayyaci Joe Ajaero kan wani zargi amma ya gaza amsa gayyatar.
A saboda haka ne jami'an DSS suka cafke Joe Ajaero yayin da yake kokarin fita zuwa Birtaniya a safiyar yau Litinin.
NLC ta yi zargin ana mata cin fuska
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kwadago ta yi Allah wadai da kama shugabanta, Joe Ajaero da jami'an DSS suka yi a birnin tarayya Abuja.
An ruwaito cewa yan kungiyar NLC sun bayyana cewa cin zarafi da barazana da gwamnatin tarayya ke musu dole a kawo karshensa a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng