'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Wani Asibiti a Kaduna, Sun Tafka Ɓarna

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Wani Asibiti a Kaduna, Sun Tafka Ɓarna

  • Ƴan bindiga sun shiga wani asibitin dakin shan magani a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna ranar Litinin
  • Shugaban rundunar ƴan banga na yankin ya ce maharan sun fara shiga wata maƙarantar sakandire kafin daga bisani su shiga asibitin
  • Har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Kaduna ko rundunar ƴan sandan jihar game da wannan hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Birnin-Gwari, Kaduna - Ƴan bindiga sun kai kazamin farmaki asibitin PHC da ke kauyen Kuyallo a ƙaramar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da ma'aikatan jinya da kuma majinyata da dama a harin na yau Litinin, 9 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari Arewa maso Yamma, sun yi garkuwa da mutane 15

Taswirar jihar Kaduna.
Yan bindiga sun yi awon gaba da majinyata a wani asibiti da ke ƙaramar hukumar Birnin-Gwari Hoto: Legit.ng
Asali: Original

The Nation ta ce har kawo yanzu da ta haɗa rahoton babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Kaduna ko rundunar ƴan sanda kan sabon harin.

Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ci tura domin baya amsa kiran waya ko sakonni.

Yadda ƴan bindiga suka shiga asibitin

An tattaro cewa maharan sun isa kauyen da karfe 9:00 na safe kuma da farko sun shiga makarantar sakandire ta gwamnati amma suka taras babu kowa.

A cewar shugaban ƙungiyar ƴan banga na yankin, Musa Alhassan, ganin babu kowa a makarantar ne ya sa ‘yan bindigar suka karkata akalarsu zuwa asibitin.

"Sun zo da niyyar farmakar ɗalibai amma da suka ga makarantar babu kowa sai suka wuce asibitin, suka ɗauki mutane," in ji shi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ta'asa a wani harin ta'addanci a Katsina

Matane nawa aka sace a harin asibitin?

Ganau sun ce maharan na ɗauke da bindigu da adduna a lokacin da suka tattara mutane suka tafi da su a asibitin ciki hada ma'aikatan jinya mata guda biyu.

Har yanzun ba a tantance yawan majinyatan da maharan suka yi garkuwa da su ba a harin wanda ya haifar da firgici da tsoro a zuƙatan mazauna garin, in ji Punch.

An cafke masu taimakon 'yan bindiga Kaduna

A wani rahoton kuma dakarun sojoji sun samu nasarar kama wasu mata da ake zargin suna haɗa baki da ƴan bindiga a jihar Kaduna.

Sojojin sun cafke matan ne guda biyu bayan sun je sayo kayayyaki ga ƴan bindiga a ƙauyen SCC da ke ƙaramar hukumar Kachia.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262