DSS: Kungiyar Kwadago Ta Shiga Damuwa an Halin da Shugabanta, Ajaero Ke Ciki

DSS: Kungiyar Kwadago Ta Shiga Damuwa an Halin da Shugabanta, Ajaero Ke Ciki

  • Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta ce ta na cikin damuwa saboda rashin sanin halin da shugabanta, Joe Ajaero ya ke ciki
  • Shugaban sashen bayanai da hulda da jama'a na kungiyar, Benson Ubah ya bayyana cewa tun bayan kama shugaban aka sa su a duhu
  • A safiyar yau ne jami'an tsaro su ka damke shugaban NLC, Joe Ajaero bayan gwamnati ta zarge shi da hannu a kokarin kifar da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta bayyana damuwa kan halin da shugabanta, Kwamred Joe Ajaero ke ciki bayan kukumar tsaron farin kaya ta DSS ta cafke shi.

Kara karanta wannan

"Ana cin zarafin 'dan adam," Amnesty int'l, Shehu Sani sun yi tir da kutsen DSS a ofishin SERAP

A safiyar yau ne wasu jami’an tsaro da ake kyautata zaton DSS ne su ka cakumo Kwamred Joe Ajaero a hanyarsa ta zuwa Birtaniya bisa gayyatar kungiyar ma’aikatan kasar.

Kungiyar NLC
NLC ta damu bisa cafke shugabanta, Joe Ajaero Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban sashen bayanai da hulda da jama’a na NLC, Benson Upah ya ce su na cikin damuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya jefa NLC cikin damuwa

Jaridar The Cable ta ce kungiyar kwadago ta NLC ta ce ta fada damuwa ne saboda babu wanda ya sanar da ita halin da shugabanta ke ciki bayan kama shi.

Jami'in hulda da jama'a na NLC, Benson Upah ne ya bayyana haka a ranar Litinin jim kadan bayan an tabbatar da jami'an tsaro sun cafke shi.

Amnesty ta magantu kan cafke shugaban NLC

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty Int'l ta yi tir da kama shugaban kungiyar kwadago na kasa (NLC), Joe Ajaero.

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito kan dalilin kama shugaban kwadago da DSS ta yi

Shugaban kungiyar reshen Najeriya, Isa Sanusi ya tabbatarwa Legit cewa abin da gwamnatin Najeriya ke yi a yanzu ya keta hakkin bil adama.

DSS ta cafke shugaban NLC

A baya mun ruwaito cewa hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta cafke shugaban kungiyar kwadago na NLC a filin jirgin Abuja a hanyarsa ta zuwa Birtaniya bisa gayyatar kungiyar yan kasuwa.

Daraktan yada labaran NLC, Benson Upah ya tabbatar da kama shugaban kungiyar, inda ya kara da cewa ba su da masaniyar inda aka kai Kwamred Joe Ajaero a lokacin da aka samu labarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.