Kama Ajaero: Yan Kwadago Sun Shiga Taron Gaggawa, Sun Tura Buƙata ga Kungiyoyi
- Kungiyar kwadago ta shiga taron gaggawa bayan jami'an DSS sun cafke shugabanta, Joe Ajaero a birnin tarayya Abuja
- Yan kwadago sun ce kama Kwamared Joe Ajaero ya sabawa dokar kasa kuma sun bukaci jami'an DSS su gaggauta sakin shi
- NLC ta ce nan ba da dadewa ba za ta sanar da yan Najeriya matakin da za ta dauka kan kama Joe Ajaero da aka yi yana shirin yin tafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta shiga taron gaggawa bayan kama shugabanta, Kwamared Joe Ajaero.
Kungiyar NLC ta yi kira na musamman ga kungiyoyin kare hakkin dan Adam da su saka ido kan abin da ke faruwa a Najeriya.
Legit ta tatttaro bayanai ne a cikin wani sako da kungiyar NLC ta wallafa a shafinta na Facebook a yau Litinin.
NCL ta bukaci a saki Joe Ajaero
Kungiyar NLC ta bukaci jami'an DSS su gaggauta sakin shugabanta, Joe Ajaero ba tare da wani sharadi ba.
NLC ta ce hakan shi ne abin da yafi dacewa kasancewar kama Joe Ajaero ba ya cikin tsarin dokar Najeriya.
NLC ta yi kira ga kungiyoyin sa kai
NLC ta yi kira na musamman ga kungiyoyin sa kai a faɗin duniya da masu kare hakkin dan Adam.
Yan kwadago sun ce ya zama dole a saka ido kan yadda nuna karfin iko ke tasowa a hankali a Najeriya a wannan lokacin.
'Yan NLC sun shiga taron gaggawa a Abuja
Punch ta wallafa cewa a yanzu haka yan kwadago sun ce sun ba dukkan jami'ansu a jihohi umarni kan zaman ko-ta-kwanan.
Sun ce nan ba da dadewa ba za su fitar da sanarwa kan matakin da za su dauka domin kama Joe Ajaero ba tare da wani laifi ba.
NLC ta yi magana kan kama Joe Ajaero
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kwadago ta yi Allah wadai da kama shugabanta, Joe Ajaero da jami'an DSS suka yi a birnin Abuja.
Yan kungiyar NLC sun bayyana cewa cin zarafi da barazana da gwamnatin tarayya ke musu dole a kawo karshensa a Najeriya cikin gaggawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng