‘Ya Isa Haka’: Yan Kwadago Sun Dauki Ɗumi bayan Kama Shugabansu

‘Ya Isa Haka’: Yan Kwadago Sun Dauki Ɗumi bayan Kama Shugabansu

  • Kungiyar kwadago ta yi Allah wadai da kama shugabanta, Joe Ajaero da jami'an DSS suka yi a birnin tarayya Abuja a yau Litinin
  • Yan kungiyar NLC sun bayyana cewa cin zarafi da barazana da gwamnatin tarayya ke musu dole a kawo karshensa a Najeriya
  • An ruwaito cewa jami'an DSS sun kama shugaban kwadago, Joe Ajaero ne yayin da yake kokarin tafiya Birtaniya domin halartar taro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta yi martani bayan jami'an DSS sun kama Joe Ajaero a yau Litinin.

Kungiyar NCL ta yi Allah wadai da lamarin kuma ta bukaci a gaggauta sake shugabanta, Joe Ajaero cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

NLC ta na son jiƙawa Tinubu aiki, ta bukaci rage kudin fetur a jerin bukatu 4

Yan kwadago
NCL ta yi maratani bayan kama Joe Ajaero. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro abin da kungiyar kwadago ta fada ne a cikin wani sako da NLC ta wallafa a shafinta na Facebook.

NLC: 'Ana cin zarafin ma'aikata a Najeriya'

Kungiyar yan kwadago ta NLC ta bayyana cewa ana cigaba da cin zarafin ma'aikata a fadin Najeriya.

NLC ta fadi haka ne bayan an kama shugaban kwadago na kasa, Joe Ajaero a birnin tarayya Abuja.

NLC ta bukaci a daina cin zarafin ma'aikata

Kungiyar kwadago ta wallafa cewa dole ne a daina cin zarafin ma'ikata a Najeriya ta hanyar kama shugabanninta.

Yan kwadago sun ce barazana da cin fuska da ake yi masu a Najeriya dole ne a tabbatar da cewa sun zo karshe.

Yanzu haka Joe Ajaero yana ina?

Kungiyar kwadago ta bayyana cewa yanzu haka ana rike da shugabanta, Joe Ajaero a ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Kara karanta wannan

"Ana cin zarafin 'dan adam," Amnesty int'l, Shehu Sani sun yi tir da kutsen DSS a ofishin SERAP

Haka zalika kungiyar ta ce an kama Joe Ajaero ne yayin da zai tafi taron yan kwadago a kasar Birtaniya.

Majalisa ta gargadi yan sanda kan Ajaero

A wani rahoton, kun ji cewa yan majalisa daga jam'iyyun adawa sun caccaki matakin rundunar yan sandan kasar nan na gayyatar shugaban NLC, Joe Ajaero.

Rundunar ta mika takardar gayyata ga shugaban NLC, Joe Ajaero bisa zargin daukar nauyin ta'addanci yayin zanga-zanga a kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng