Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Ranar Sake Zama da ASUU

Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Ranar Sake Zama da ASUU

  • Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa domin cimma matsaya da kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta fadi ranar ganawa ta gaba
  • Mataimakin shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ya tabbatar da cewa za a gana da gwamnati a ranar Laraba, 11 Satumba, 2024
  • Farfesa Piwuna ya ce a taron baya da su ka gudanar da kwamitin gwamnatin karkashin jagorancin Ministan Ilimi, an kafa kwamitoci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) ta tabbatar da cewa gwamnati da kusoshin ASUU za su sake ganawa a ranar Laraba, 11 Satumba, 2024.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin mai: Gwamnati ta fadi lokacin da fetur zai wadata a fadin Najeriya

Wannan na zuwa bayan kungiyar ta yi barazanar sake tsunduma yajin aiki matukar gwamnatin Tinubu ta ci gaba da watsi da yarjejeniyar da aka cimma a baya.

Kungiyar ASUU
An sake sa ranar ganawa tsakanin ASUU da gwamnati Hoto: ASUU
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa a zaman da aka yi tsakanin ASUU da kwamitin gwamnati karkashin jagorancin Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, an samu nasara

ASUU da gwamnati: An kafa kwamiti

Mataimakin shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Chris Piwuna ya bayyana cewa an kafa kwamitin da zai yi duba kan batun IPPIS da sauran matsalolin albashin da ake bin gwamnati.

Ya ce an cimma matsayar ne bayan taron baya-bayan nan da ya gudana, karkashin jagorancin Ministan Ilimi, Tahir Mamman.

"Batun ASUU dadadde ne," Gwamnati

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa wasu daga cikin bukatun da ASUU ke neman gwamnati ta biya mata sun dade, wasu tun daga shekarar 1981 ake neman a samar da su.

Kara karanta wannan

Ana kuka da tsadar mai, Gwamna a Arewa ya cire tuta wurin kawowa al'umma sauki

Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya kara da cewa amma da yawa daga cikin bukatun da ASUU ke bukata, tuni shugaban kasa ya fara kokarin magance su.

Gwamnati, ASUU sun tattauna

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) sun cimma matsaya bayan ganawa da su ka yi a kokarin hana yajin aikin gama gari.

Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya bayyana cewa shugabannin ASUU sun amince a sake zama domin ci gaba da duba matsalolin da su ka nemi gwamnatin tarayya ta magance masu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.