Jami'an DSS Sun Cafke Shugaban Kungiyar NLC na Kasa, an Samu Bayanai
- Jami'an hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) sun kama shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) , Joe Ajaero a birnin tarayya Abuja
- Jami'an na DSS sun cafke Ajaero ne da safiyar ranar Litinin a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja yayin da shirin barin Najeriya
- Daraktan yaɗa labarai na ƙungiyar NLC ya tabbatar da cafke Joe Ajaero inda ya ƙara da cewa bai san inda aka tafi da shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun cafke shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero.
Jami'an na hukumar DSS sun cafke Joe Ajaero ne da safiyar ranar Litinin, 9 ga watan Satumban 2024.
Jami'an DSS sun cafke Joe Ajaero
Vanguard ta rahoto cewa an kama shugaban na NLC ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Joe Ajaero na shirin shiga jirgi zuwa ƙasar Ingila, UK, domin halartar wani taro lokacin da jami'an hukumar DSS suka ɗauke shi.
Ko da yake har yanzu babu cikakken bayani game da kama shi da dalilan da suka sa aka kama shi, majiyoyi sun ce an miƙa shi ga hukumar leƙen asiri ta ƙasa (NIA).
An yi ran da shugaban NLC zai je waje
A cewar majiyoyin, Ajaero zai halarci taron ƙungiyar ƴan kasuwa (TUC), wanda za a gudanar a ƙasar Birtaniya a yau Litinin.
Kamun na Joe Ajaero na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ya amsa gayyatar da ƴan sanda suka yi masa kan zargin ɗaukar nauyin ta'addanci.
NLC ta tabbatar da cafke Ajaero
Tashar Channels tv ta ce daraktan yaɗa labarai na ƙungiyar NLC, Benson Upah ya tabbatar mata da cafke Joe Ajaero.
Benson Upah ya bayyana cewa bai san inda aka kai Ajaero ba amma ya turo saƙo inda ya tabbatar da cewa jami'an DSS ne suka cafke shi.
NLC ta caccaki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta caccaki gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu kan halin ƙuncin da ake ciki a Najeriya.
NLC ta bayyana gwamnatocin baya na Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari sun fi na Shugaba Tinubu dama-dama wajen tausayawa talaka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng