An Shiga Ruɗani kan Wajen da ake Sayar da Buhun Shinkafar Tinubu a N40,000
- A makon da ya wuce gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta kaddamar da fara sayar da buhun shinkafa a kan N40,000
- Ministan noma, Abubakar Kyari ya ce an kawo shirin ne domin saukakawa al'ummar Najeriya kan halin wahalar da ake ciki
- Sai dai yan Najeriya a birnin tarayya Abuja sun koka kan yadda suka gaza gano wajen da gwamnati ke sayar da shinkafar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Yan Najeriya sun bayyana halin da ake ciki bayan gwamnatin tarayya ta kaddamar da sayar da buhun shinkafa a N40,000.
Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari ne ya kaddamar da sayar da shinkafar.
Punch ta wallafa yadda ta zanta da wasu mazauna Abuja inda suka gaza gano wajen da ake sayar da shinkafar har yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Eleojo: 'Na saye buhun shinkafa a N84,000'
Wata mazauniyar Kuje a birnin tarayya Abuja ta ce su dai sun ji gwamnati za ta sayar da shinkafa a N40,000 amma ba su san a ina za su samu ba balle su saye ta.
Saboda haka ne ma Eleojo Yunusa ta ce dole sai da ta je kasuwa ta saye shinkafa a N84,000 kuma a hakan ma an ce farashin sari ne.
Wata mata ta ce a talabijin suka ji labari
Wata mata da ke zaune a Bwari a birnin tarayya ta ce su dai sun ga gwamnati na tallata sayar da shinkafa a talabijin ne kawai.
Legit ta ruwaito cewa matar mai suna Maman Twins ta ce har yanzu ba su san wajen da ake sayar da shinkafar ba a birnin tarayya Abuja.
Salami: Ba mu da tabbas kan shinkafar Tinubu'
Wani mazaunin birnin tarayya, Salami Taiwo ya ce shi ba shi da tabbas a kan cewa za a sayar da shinkafar da gaske.
Salami Taiwo ya ce ya fadi haka ne saboda yadda gwamnatin tarayya ke abubuwan da babu alamar sauki a cikinsu.
Sharadin sayen shinkafar Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana shirin fara sayar wa ma'aikatanta buhun shinkafa mai girman kilo 50 kan N40,000.
Gwamnatin za ta fara sayarwa ma'aikata tan 30,000 na shinkafar kan farashi mai rangwame saboda tsadar rayuwa amma sai wanda yake da NIN.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng