'Na Kashe N20000 a Rana 1': Jigon APC Ya Fadawa Tinubu babbar Illar Karin Kudin Wuta

'Na Kashe N20000 a Rana 1': Jigon APC Ya Fadawa Tinubu babbar Illar Karin Kudin Wuta

  • Daya daga cikin 'yan a-mutun gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ya fara kokawa kan karin kudin wutar lantarki da aka yi
  • Joe Igbokwe ya ce a rana daya kacal ya sha wutar N20,000 a wani dan karamin ofishinsa a Surulere, abin da ya ce ya yi yawa
  • A zantawarmu da Janare Bature, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta wadatar da wuta a kasar wanda zai kawo bunkasar kasuwanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Joe Igbokwe, jigo a jam’iyyar APC, ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya duba yiyuwar janye karin kudin wutar lantarki da aka yi a kasar.

Joe Igbokwe, babban mai goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ya ce karin kudin wutar zai durkusar da ‘yan kasuwa da dama, don haka akwai bukatar janye shi.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa na neman muƙamin mataimaki a 2027? ya yi magana

Jigon APC ya yi magana kan karin kudin wutar lantarki a Najeriya
Jigon APC, Joe Igbokwe ya roki Tinubu ya janye karin kudin wutar lantarki. Hoto: Joe Igbokwe
Asali: Facebook

Jigon APC ya sha wutar N20,000

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a karshen makon nan, Igbokwe ya koka da cewa a rana yana shan wutar N20,000, wanda ya ke ganin ya wuce kima.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce yana da wani karamin ofishi a Surulere, inda ya sanya masa kimanin 300units na lantarki amma suka shanye wutar a rana daya kacal.

Don haka jigon na APC ya bukaci gwamnatin shugaban kasa Tinubu da ta sake duba batun karin kudin wutar lantarkin.

"A janye karin kudin wutar lantarki" - Igbokwe

Igbokwe ya bayyana cewa:

“PBAT, don Allah a duba batun karin kudin wutar lantarki a Najeriya. Za a durkusar da 'yan kasuwa idan gwamnati ba ta hanzarta daukar mataki ba.
"Ina da dan karamin ofishi a Surulere, mai dauke da AC guda 7, jiya muka sanya wutar N20,000 amma abin mamaki mun karar da ita a wannan ranar kacal."

Kara karanta wannan

Mai garkuwa da mutane ya yanke sassan jikin budurwa bayan karbar kudin fansa

Jigon na APC ya ce N20,000 ta saya masu 300unit na wutar lantarki amma ta kare a cikin kwana daya, yana mai rokon Tinubu da ya janye karin kudin wutar da aka yi.

"Ba ma samun wuta" - Janare

A zantawarmu da Janare Bature, daga jihar Katsina, ya koka kan cewa gwamnatin tarayya ta kara kudin wutar ne ba tare da la'akari da cewa wutar ba ta samuwa a yanzu ba.

A cewar Janare, duk da cewa karin ya shafi wadanda ke a tsarin 'Band A' ne sai dai ya nuna bukatar gyara wutar ta zama wadatacciya a fadin kasar ba ga wani rukuni kadai ba.

"Idan wuta ta wadata, kamfanoni da dama za su dawo aiki, babu wanda zai damu da karin kudin fetur, sannan jama'a za su samu ayyukan yi.
"Ware wani bangare a ce shi kadai zai samu wuta ta awa 24 kamar bangaranci ne, ya kamata ace an ba kowanne dan kasa zabi, domin akwai masu sana'ar da za su iya biya."

Kara karanta wannan

"Zaluncin gwamnatin Tinubu ya fi na soja:" Atiku ya soki yadda ake murkushe kungiyoyi

- A cewar Janare Bature.

Majalisa ta ba NERC sabon umarni

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilai ta bukaci hukumar NERC da ta dakatar da aiwatar da sabon karin kudin wutar da ta yi ga 'yan 'Band A.'

Nkemkanma Kama, dan majalisar wakilai na jam’iyyar Labour Party (LP) daga jihar Ebonyi ne ya gabatar da kudurin bukatar jama'a gaban majalisar kan dakatar da NERC daga aiwatar da karin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.