Tsohon Minista Ya Gargadi Tinubu a kan Karbo Bashi daga Kasar Sin, Ya Fadi Dalili

Tsohon Minista Ya Gargadi Tinubu a kan Karbo Bashi daga Kasar Sin, Ya Fadi Dalili

  • Tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, Bolaji Akinyemi ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan kan karbar bashin Sin
  • Bolaji Akinyemi ya ce Sin ba za ta rufawa Najeriya asiri idan ta kwabe ba, yana mai buga misali da rikicin kasar da wani kamfanin Sin
  • Kasar Sin na bin Najeriya bashin kusan 84% na dukkanin bashin dala biliyan biyar da ake bin Najeriya, wanda ya haura dala biliyan hudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon ministan harkokin kasashen waje, Bolaji Akinyemi, ya gargadi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta yi taka-tsan-tsan da karbo rancen kudi daga kasar Sin.

Akinyemi, ya bayyana cewa bai kamata Shugaba Tinubu ya sake maimaita kura-kuran da gwamnatocin baya suka yi a kasar nan ba.

Kara karanta wannan

'Buhari ya na Daura ya na yi wa 'yan Najeriya dariyar halin da suke ciki' inji Kakakin Jonathan

Tsohon ministan Najeriya na gargadi Tinubu kan karbo bashi daga kasar Sin
Tsohon ministan ya nemi Tinubu ya yi taka-tsan-tsan wajen karbo bashi daga Sin. Hoto: @Onyeani_Kalu
Asali: Twitter

Tsohon ministan harkokin kasashen wajen, wanda ya rike mukamin daga shekarar 1985 zuwa karshen 1987 ya gargadi Tinubu ne a cikin shirin siyasa na Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ayi taka-tsan-tasan da Sin" - Bolaji

Bolaji Akinyemi, ya ce:

"Tabbas, ya zama wajibi mu yi taka-tsan-tsan amma kar mu ware kasar Sin kadai. Amurka na binmu bashi, akwai kananun kasashe da ke binmu bashi.
Wata guda gabanin gudanar da taron koli na kasashen Afrika da Sin, an fara kame kadarorin Najeriya a fadin duniya bisa taimakon wani kamfani na kasar Sin.
"Saboda haka, kasar Sin ba za ta rufa mana asiri a idon duniya ba, dole ne mu yi taka-tsan-tsan, ba ga kasar Sin kadai ba, har ma da sauran kasashen da za mu yi mu'amala da su."

Bashin da Sin ke bin Najeriya

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaba Tinubu da shugaban kasar Sin, Xi Jinping, suka yi musayar ra'ayi kan hanyoyin karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Kara karanta wannan

"Mutane za su wahala": Atiku ya yi adawa da shirin kara hajari, ya gargadi Tinubu

An rahoto cewa Najeriya na da bashin manyan kasashen duniya biyar a kanta: Sin, Faransa, Japan, Indiya da Jamus.

Kasar Sin ita ce kasar da ta fi kowacce kasa ba Najeriya lamuni, a cewar ofishin kula da basussuka (DMO).

Kasar Sin na bin Najeriya bashin kusan 84% na dukkanin bashin dala biliyan 5 da ake bin Najeriya, wanda ya haura dala biliyan 4.

Tinubu ya shilla kasar Sin

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bar babban birnin tarayya Abuja zuwa kasar Sin inda zai kai ziyarar aiki.

Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu zai gana da Shugaban kasar Sin, Xi Jinping da kuma yan kasuwa, yayin da kuma zai tsaya wata yar takaitacciyar ziyara a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.