"Ba Cire Tallafi Za a Yi ba": Kwankwaso Ya Fadi Tanadinsa kan Badakala a Bangaren Mai

"Ba Cire Tallafi Za a Yi ba": Kwankwaso Ya Fadi Tanadinsa kan Badakala a Bangaren Mai

  • Jigon jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan lamarin cire tallafin man fetur a Najeriya
  • Kwankwaso ya bayyana cewa shi tun yana neman mulkin Najeriya sun tsara yadda za su yi kan maganar tallafin mai
  • Tsohon gwamnan Kano ya ce akwai hanyoyi da yawa na dakile barnar da ake tafkawa ba sai an cire tallafin man fetur ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso ya sake magana kan cire tallafin man fetur.

Kwankwaso ya ce a cikin maidu'in da suka fitar na ayyukan alheri da za su yiwa Najeriya a bayyane yake.

Kara karanta wannan

"PDP ta mutu": Ana rade radin haɗaka, Kwankwaso ya bugawa jam'iyyar kusa a kai

Kwankwaso ya fadi shirinsa kan maganar cire tallafin man fetur
Sanata Rabi'u Kwankwaso ya magantu kan maganar cire tallafin mai. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Twitter

Cire tallafi: Kwankwaso ya fadi shirinsa

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren sadarwa, Abdullahi Ibrahim ya wallafa a shafin X.

Kwankwaso ya ce ba tallafin mai ba ne ya kamata a fara tabawa ba akwai wasu abubuwa da dole sai an dakile su.

Jigon NNPP ya ce dole gwamnati ce kadai za ta dakile almundahana da ta'asa da ake yi game da tallafin mai.

" Ku je ku duba maidu'inmu kan maganar cire tallafin mai, mu a cikin littafinmu yana nan."
"Kuma na tabbata in ba dukanku ba to tabbas wasunku suna da shi a tare da su"
"Abin da muka ce shi ne ka da ka taba tallafi, ka tafi inda ake badakala da ta'asa ka dakile."

Kara karanta wannan

An soki Barau Jibrin kan karbar mutane zuwa APC alhali ana kukan kuncin rayuwa

- Rabi'u Musa Kwankwaso

Kwankwaso ya fadi hanyar dakile almundahanar mai

Kwankwaso ya ce babu wanda zai iya dakile karairayi da ake yi kan tallafin mai sai gwamnati.

Ya ce ana kawo jirgin ruwa biyu zuwa uku amma sai a rubuta a ce guda daya ne duk wannnan gwamnati ce za ta iya maganinsu.

Kwankwaso ta fadi yadda ya kassara PDP

Kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana yadda ya kashe jam'iyyar PDP murus bayan ya fice.

Kwankwaso ya ce a yanzu PDP macecciya ce babu wani tasiri da ta ke da shi da ya saura a gare ta yayin da ake tunkarar zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.