Jigon APC Ya Gayawa Shugaba Tinubu Gaskiya kan Tsadar Rayuwa

Jigon APC Ya Gayawa Shugaba Tinubu Gaskiya kan Tsadar Rayuwa

  • Olatunbosun Oyintiloye ya fito ya koka kan halin ƙunci da tsadar rayuwar da ƴan Najeriya suke fama da shi a halin yanzu
  • Jigon na jam'iyyar APC a jihar Osun, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ɗauki matakan sauƙaƙawa talakawa
  • Ya bayyana cewa ya kamata Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin cikin sauri domim tsamo mutane daga halin da suka tsinci kansu a ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Osun - Wani jigo a jam'iyyar APC a jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ba Shugaba Bola Tinubu shawara.

Olatunbosun Oyintiloye ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta cire ƴan Najeriya daga cikin halin ƙuncin da suke ciki.

Jigo a APC ya ba Tinubu shawara
Jigon APC ya bukaci Tinubu ya tausayawa talaka Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

"Ƴan Najeriya na ji a jika", jigon APC

Kara karanta wannan

Ajuri Ngelale: Kura kurai 2 da suka sa hadimin Tinubu ya ajiye aikinsa

Jaridar The Punch ta rahoto jigon na APC ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a birnin Osogbo babban birnin jihar Osun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olatunbosun Oyintiloye ya nuna cewa ƴan Najeriya na shan wuya wanda hakan ya sanya dole shugaban ƙasan ya ɗauki matakan kawo musu ɗauki, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Wace shawara aka ba Tinubu

Duk da ya nuna ƙwarin gwiwar cewa Shugaba Tinubu zai iya rage wahalun da ƴan Najeriya ke sha, ya ba da shawarar cewa ya kamata a bi hanyoyin da za su tabbatar da hakan cikin gaggawa.

"Ko tantama babu cewa shugaban ƙasa yana bakin ƙoƙarinsa domin rage raɗaɗin da ake fama da shi, amma ya kamata a bi hanyar da za a cimma hakan cikin sauri."
"Ya kamata shugaban ƙasa ya tabbatar da cewa an cire duk wasu abubuwan da suka kawo jinkiri wajen aiwatar da shirye-shiryen da za su amfani talakawa."

Kara karanta wannan

Ajuri Ngelale: 'Yan Najeriya sun yi martani kan ajiye aikin hadimin Tinubu

"Matsalar tattalin arziƙin da mutane ke fuskanta ta yi tsanani a halin yanzu, dole ne shugaban ƙasa ya ɗauki mataki cikin gaggawa.

- Olatunbosun Oyintiloye

Atiku ya caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya ce karin harajin VAT da ake shirin yi a kasar nan zai zama wata wuta da za ta cinye rayuwar al’ummar Najeriya.

Atiku ya ce Shugaba Bola Tinubu tare da masu ba shi shawara, sun yanke shawarar kara harajin VAT daga 7.5% zuwa 10%, duk da sanin cewa NNPCL ya kara kudin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng