Gwamnatin Kano Ta Dage Ranakun Komawa Makaranta, Ta Fadi Dalili
- Gwamnatin jihar Kano ta sanar da ɗaukar matakin ɗage ranakun da za a koma makarantun firamare da na gaba da su a jihar
- Ma'aikatar ilmi ta jihar wacce ta sanar da ɗage ranakun komawa makarantar ta bayyana cewa ta yi hakan ne saboda wasu dalilai na gaggawa
- Ta bayyana cewa za ta sanar da sabuwar ranar da ɗalibai za su koma makarantu domin ci gaba da karatu a nan gaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ɗage ranar da za a koma makarantun firamare da na gaba da firamare domin zangon karatun 2024/2025 har sai baba ta gani.
Gwamnatin Kano ta ce ta ɗauki matakin ne saboda dalilai na gaggawa, duk da dai ba ta bayyana dalilan na gaggawar ba.
Daraktan wayar da kan jama'a na ma'aikatar ilmi, Balarabe Kiru, ne ya sanar da ɗage ranar komawa makarantun a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kano, cewar rahoton jaridar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, kwamishinan ilimi, Umar Doguwa, ya ce wasu dalilai na gaggawa da ba a bayyana ba ne suka tilasta yanke hukuncin, rahoton ICIR ya tabbatar.
Yaushe za a koma makarantu a Kano?
Balarabe Kiru ya ambato Umar Doguwa na cewa nan ba da daɗewa ba ma’aikatar za ta bayyana sabuwar ranar da za a koma makarantun.
"Ina so na sanar da ɗalibai da iyayen yara cewa an ɗage sanarwar da aka bayar tun da farko kan komawa makaranta a ranakun 8 da 9 ga watan Satumban 2024 cewa an ɗage ta."
"Hakan ya faru ne saboda wasu dalilai na gaggawa da za su taimaka wajen samar da ingantaccen yanayin karatu ga yaran mu."
"Za a sanar da sabuwar ranar da za a koma makaranta nan ba da jimawa ba."
- Umar Doguwa
Balarabe Kiru ya buƙaci mutanen da abin ya shafa musamman ɗalibai da iyayen yara da su yi haƙuri da wannan sauyin da aka samu.
Majalisa ta amince da ƙarin kasafin kuɗin Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin jihar kano ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kudin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika mata.
Ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗin ya zarce Naira Biliyan 99 domin sanya shi a cikin kasafin kudin shekarar da muke ciki
Asali: Legit.ng