Ajuri Ngelale: Tinubu Ya Yi Magana bayan Hadiminsa Ya Ajiye Aiki, Ya Dauki Mataki

Ajuri Ngelale: Tinubu Ya Yi Magana bayan Hadiminsa Ya Ajiye Aiki, Ya Dauki Mataki

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da karbar takardar murabus da hadiminsa, Ajuri Ngelale ya yi a jiya Asabar
  • Tinubu ya godewa Ngelale game da gudunmawar da ya bayar tare da yi masa fatan alheri da kuma iyalansa
  • Wannan na zuwa ne bayan ajiye aiki da Ngelale ya yi saboda dalilai na rashin lafiyar iyalansa da ya yi tsanani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya karbi ajiye aiki da hadiminsa, Ajuri Ngelale ya yi a jiya Asabar 7 ga watan Satumbar 2024.

Tinubu ya jajantawa Ngelale tare da nuna damuwa kan halin rashin lafiya da ya tilasta shi ajiye aikin.

Kara karanta wannan

"Ba rashin lafiya ba ne": An fadi ainihin 'dalilin' Ajuri Ngelale na ajiye aikinsa

Tinubu ya yi magana bayan Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa
Tinubu ya yi wa Ajuri Ngelale fatan alheri da kuma tarun godiya. Hoto: @DOlusegun.
Asali: Twitter

Tinubu ya yi magana game da Ajuri

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa na musamman, Dada Olusegun ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce Tinubu ya yi masa fatan alheri tare da yin addu'ar samun sauki ga iyalansa cikin gaggawa.

Tinubu ya kuma yi godiya ga Ngelale game da gudunmawar da ya bayar lokacin da ya ke hadiminsa.

Daga bisani shugaban ya roki yan Najeriya su ba Ngelale sirri da shi da iyalansa domin samun sauki cikin gaggawa.

Tinubu ya godewa Ajuri Ngelale kan kokarinsa

"Shugaban kasa ya karbi takardar ajiye aiki da Ajuri Ngelale ya yi kuma ya tausaya masa kan halin da ya tilasta shi murabus."
"Yayin da ke yi masa fatan alheri ya yi addu'ar samun sauki ga iyalan nasa cikin gaggawa."

Kara karanta wannan

"Zai ɗan yi ƙiba": Shehu Sani ya yi martani bayan hadimin Tinubu ya ajiye aikinsa

"Tinubu ya yi godiya matuka game da gudunmawar da Ngelale ya bayar domin cigaban Najeriya baki daya."

- Bola Tinubu

Hadimin Tinubu, Ajuri Ngelale ya ajiye aiki

Kun ji cewa babban hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa a jiya Asabar 7 ga watan Satumbar 2024.

Ngelale ya ajiye aikin ne domin ba iyalansa kulawa na musamman wanda ya ce lamarin ya yi tsanani da ya tilasta shi ajiye aikin nasa.

Tsohon hadimin Tinubu ya tabbatar da mika takardar murabus din ne ga shugaban ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.