"Buhari ma Ya Fi Shi": NLC Ta Fadi Gwamnatoci 2 da Suka Ɗara Mulkin Tinubu

"Buhari ma Ya Fi Shi": NLC Ta Fadi Gwamnatoci 2 da Suka Ɗara Mulkin Tinubu

  • Kungiyar kwadago ta NLC ta fadi gwamnatoci biyu da suka dara na Shugaba Bola Tinubu a tsarin tattalin arziki
  • Kungiyar ta ce gwamnatocin Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari sun yiwa na Tinubu fintinkau kan tsare-tsare masu kyau
  • Wannan na zuwa ne bayan wasu matakai da Tinubu ke dauka na tattalin arziki wadanda suka jefa al'umma cikin matsi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta NLC ta caccaki gwamnatin Bola Tinubu a Najeriya.

NLC ta ce gwamnatocin Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari sun fi na Tinubu dama-dama.

NLC ta fadi gwamnatocin da suka fi na Tinubu tsare-tsare
Kungiyar NLC ta yaba gwamnatocin Jonathan da Buhari kan na Tinubu. Hoto: @DOlusegun.
Asali: Twitter

NLC ta yaba Jonathan, Buhari kan Tinubu

Kara karanta wannan

Karin farashin mai: Tinubu ya fadi kasar da yake fatan Najeriya ta zama, ya ba da shawara

Kakakin kungiyar, Benson Upah shi ya bayyana haka yayin hira da jaridar Daily Trust a jiya Juma'a 6 ga watan Satumbar 2024.

Upah ya ce gwamnatocin da suka wuce sun dara na Tinubu kan tsare-tsaren tattalin arziki, cewar rahoton Punch.

Ya ce Buhari ya na da saukin kai saboda ya yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da samun sauki a kasa.

Har ila yau, Upah ya ce Tinubu ya yi gaban kansa wurin cire tallafin mai ba tare da duba wahalar da za a shiga ba.

Kakakin kungiyar ya kuma kwatanta darajar Naira zuwa dala a lokacin mulkin Jonathan da kuma Tinubu.

NLC ta yabawa Buhari kan inganta ma'aikata

"Ina fadawa mutane masu cewa Buhari ya fi Tinubu muni ba haka ba ne, tsohon shugaban yana da saukin kai mu a wurinmu kungiyar kwadago."
"Ya yi kokari sosai saboda zuwansa ya ba jihohi kudi domin biyan basukan albashi da kuma fansho."

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi nasarorin da ya samu a China, ya bayyana amfanin kara kudin mai

"Muna cewa Jonathan ya yi kuskure, yanzu ku duba yadda abubuwa suke sake lalacewa kullum kara baya muke yi."

- Benson Upah

Kudin mai: Ƙungiya ta caccaki NLC

Kun ji cewa Kungiyar The Citizens for Democratic Dividends ta caccaki shugaban NLC, Joe Ajaero kan sukar Bola Tinubu game da farashin mai.

Kungiyar ta ce Ajaero kan shi kawai ya sani ba wai ta yan Najeriya yake yi ba inda ta ce shi ya yaudari yan kasar kan karin albashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.