Ana Dab da Zabe Gwamna Ya Yi Sababbin Nade Nade 300 a Gwamnatinsa
- Gwamnan jihar Ondo da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, Lucky Aiyedatiwa ya sake zaɓo wasu mutane ya ba su muƙamai a gwamnatinsa
- Gwamnan ya naɗa sababbin hadimai mutum 344 waɗanda za su riƙa taimaka masa wajen gudanar da mulkin jihar
- Sababbin hadiman waɗanda aka zaɓo daga ƙananan hukumomi 18 na jihar sun haɗa da mataimaka na musamman da manyan mataimaka na musamman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya yi sababbin naɗe-naɗe a gwamnatinsa.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya amince da naɗa ƙarin hadimai 344 a matsayin mataimaka na musamman da kuma manyan mataimaka na musamman.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Ebenezer Adeniran.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Aiyedatiwa ya nada hadimai
Jaridar The Guardian ta ce naɗe-naɗe sun haɗa da manyan mataimaka na musamman guda 28 da mataimaka na musamman guda 316.
A cewar sanarwar, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi naɗe-naɗen ne domin ci gaba da ƙoƙarin inganta sha’anin mulki da matso da gwamnati kusa da al'ummar jihar.
Sanarwar ta ce naɗe-naɗen sun shafi ƙananan hukumomi 18 da kuma mazaɓu 203 da ke jihar.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa, a cikin sanarwar, ya buƙaci sababbin hadiman da aka naɗa da su yi amfani da ƙwarewarsu da sadaukar da kansu wajen yiwa al’ummar jihar hidima.
Karanta wasu labaran kan Gwamna Aiyedatiwa
- Gwamnan APC ya bijirewa umarnin kotun koli, ya nada ciyamomin rikon kwarya
- Iyayen marayu, mata sun tsunduma zanga zanga, sun fadi yadda su ke rayuwa a Ondo
- "Babu wanda ya tsira": Miyagu sun fasa ofishin gwamnan APC, sun yashe kaya
Gwamna Aiyedatiwa zai biya albashin N70,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin jihar Ondo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Lucky Aiyedatiwa, ta amince da biyan N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne biyo bayan rattaɓa hannu kan ƙudirin dokar mafi ƙarancin albashin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi.
Asali: Legit.ng