Gwamna Ya Fallasa Yadda Shugaban Al'umma Ya Karbi Kudi Aka Hallaka Mutane
- Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ta dade tana ciwa jihar tuwo a ƙwarya
- Gwamna Radda ya bayyana cewa akwai wani wakilin shugaban al'umma da ya karɓi kuɗi a hannun ƴan bindiga ya ba su dama suka halaka mutane 30
- Gwamnan ya bayyana cewa a shirye gwamnatinsa take ta ba jama'a taimakon da suke buƙata domin kare kansu daga hare-haren ƴan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi magana kan matsalar ƴan bindiga da ake fama da ita a jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa wasu daga cikin shugabannin al'umma na taimakawa wajen matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Gwamna Radda ya bayyana hakan ne a garin Daura a wani taron tattaunawa da al'umma kan abubuwan da suke so gwamnati ta yi a kasafin kuɗin 2025, cewar rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Radda ya ce kan rashin tsaro a Katsina?
Gwamnan ya bayyana cewa a shirye gwamnatinsa take domin tallafawa al'umma su kare kansu daga ƴan bindiga, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.
Gwamna Radda ya koka kan yadda shugabannin al’umma suke haɗa kai da ƴan bindiga domin kai hari ga jama'a saboda abin duniya.
"Akwai wakilin mai unguwa da ya karɓi Naira 700,000 daga hannun ƴan bindiga ya ba su damar shiga yankinsa suka kashe kusan mutane 30."
"Akwai mata da aka kama, akwai malamin makarantar da ke zama mai ba su bayanai. Kusan kowane ɓangare na al'umma na da hannu a wannan matsalar."
- Gwamna Dikko Radda
Gwamna Radda ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta kafa rundunar tsaro ta KSWC tare da basu kayan aiki domin yaƙi da matsalar rashin tsaro a jihar.
Gwamna Radda ya shawarci mutanen Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina su ɗauki matakan kare kansu daga hare-haren ƴan bindiga.
Gwamna Radda ya kuma buƙaci malaman addinin Musulunci da su faɗakar da mutane game da muhimmancin kare kai kamar yadda Musulunci ya tanada.
Asali: Legit.ng