Karin Kuɗin Mai: Tinubu Ya Faɗi Ƙasar da Yake Fatan Najeriya Ta Zama, Ya ba da Shawara

Karin Kuɗin Mai: Tinubu Ya Faɗi Ƙasar da Yake Fatan Najeriya Ta Zama, Ya ba da Shawara

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana yadda ya ke kokarin inganta Najeriya ta dawo kamar kasar China
  • Tinubu ya ce dole sai an dauki tsauraran matakai na tattalin arziki kafin samun cigaba kamar misalin China
  • Ya bukaci yan Najeriya mazauna China da su kasance jakadu na kwarai domin kare martabar kasarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kasar China - Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi magana kan karin kudin mai da aka samu a Najeriya.

Bola Tinubu ya ce dole ne ya sanya shi daukar matakai masu tsauri domin samun cigaba a kasar.

Tinubu ya sake magana kan karin farashin man fetur a Najeriya
Bola Tinubu ya kare matakin karin farashin man fetur a Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya fadi hanyar inganta Najeriya

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren sadarwa, Ajuri Ngelale ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi nasarorin da ya samu a China, ya bayyana amfanin kara kudin mai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce dole ne yan Najeriya su zama na gari da kuma tsari kamar yadda kasar China ta ke.

Ya ce China ce Najeriya ya kamata ta yi koyi da ita amma dole sai an dauki tsauraran matakai da za su kawo hakan.

Tinubu ya kare matakin karin farashin mai

"Najeriya tana kan hanya mai kyau na cigaba, muna daukar tsauraran matakai, misali za ku iya samun labari daga gida kan tsadar man fetur."
"Amma, ya zamu yi? ta ya za mu samar da hanyoyi masu kyau irin yadda ku ke da su a nan? Ku na ganin yadda wuta ta inganta a nan da ruwa da kuma makarantu masu inganci "
"Mecece hanya mafi sauki da za mu samu cigaba idan har ba mu dauki tsauraran matakai ba da yan kasa za su jin dadi?"

Kara karanta wannan

'Fir'aunanci ne,' Malamin addini ya dura kan gwamnatin Tinubu a kan tashin man fetur

- Bola Tinubu

Tinubu ya yi magana kan karin kudin mai

Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya bukaci yan Najeriya mazauna China da su tabbatar da sun wakilci kasarsu a ketare

Tinubu ya fadi irin nasarorin da ya samu yayin ziyarar kwanaki da ya yi kasar China inda ya sake rokon yan Najeriya

Shugaban ya bayyana amfanin karin kudin mai inda ya ce ba tare da samun kudin shiga ba, babu damar yin ayyukan alheri.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.