'Ana Yunwa,' Malamin Addini Ya Tsage Gaskiya a gaban Jiga Jigan APC a Abuja

'Ana Yunwa,' Malamin Addini Ya Tsage Gaskiya a gaban Jiga Jigan APC a Abuja

  • Rabaran Matthew Hassan Kukah ya yi kira ga gwamnatin tarayya a rage kudin man fetur da aka kara da ya kara tsada
  • Faston ya ce a halin yanzu yan Najeriya na fama da yunwa saboda haka ya kamata a tausaya musu a rage kudin fetur
  • Hakan ya faru ne yayin da Rabaran Kukah ya hadu da jiga jigan jami'yyar APC a yayin wani taro a birnin tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shahararren malamin addinin Kirista, Rabaran Matthew Hassan Kukah ya yi kira kan rage kudin man fetur.

Rabaran Mathew H. Kukah ya yi kiran ne duba da yadda yan Najeriya ke shan wahala bayan an kara kudin man fetur.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi nasarorin da ya samu a China, ya bayyana amfanin kara kudin mai

Kukah
Rabaran Kukah ya bukaci a rage kudin mai. Hoto: @NigeriaGov, @Imranmuhdz
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Rabaran Kukah ya fadi maganar ne a gaban jagororin APC a birnin tarayya, Abuja.

Mathew Kukah ya bukaci a rage kudin mai

Babban Malamin addinin Kirista, Rabaran Kukah ya ce a halin yanzu 'yan Najeriya na fama da tsananin wahalar rayuwa.

A karkashin haka ya buƙaci shugabannin APC a Najeriya su rage kudin man fetur ko talaka zai samu sauƙin rayuwa a kasar nan.

Jiga jigan APC da Kukah ya yiwa magana

A gaban shugabannin APC, ya ce yan Najeriya na jin yunwa kuma yana da matukar muhimmanci a duba yanayin da suke ciki.

Cikin wadanda Rabaran Kukah ya yi wa magana yayin taron akwai shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Vanguard ta wallafa cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume na wajen.

Kara karanta wannan

'Fir'aunanci ne,' Malamin addini ya dura kan gwamnatin Tinubu a kan tashin man fetur

Rabaran Kukah ya bukaci shugabannin da su yi amfani da dimokuraɗiyya wajen kawo karshen matsalolin Najeriya.

An bukaci rage kudin mai a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa karin kudin man fetur na cigaba da jawo suka ga gwamnati musamman daga talakawa da jam'iyyun adawa.

'Yan majalisun tarayya sun bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta dawo da farashin man fetur yadda yake domin saukakawa al'ummar Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng