Matar Tinubu Ta Raba Miliyoyi a Arewacin Najeriya, Za a yi Rabo a Dukkan Jihohi
- Matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta raba miliyoyin kudi ga mata a jihar Zamfara domin bunkasa ƙananan sana'o'i
- An ruwaito cewa mata 1,000 ne suka samu kyautar tallafin a wannan karon yayin da matar shugaban kasar ta samu wakilci
- Matar shugaban kasar ta tabbatar da cewa za ta zagaya dukkan jihohin Najeriya domin raba kudin ga mata masu sana'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Matar mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta ba mata tallafin kudi a jihar Zamfara.
An ruwaito cewa Oluremi Tinubu ta raba zunzurutun kudi har N50m ga mata domin bunkasa kananan sana'o'i.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa matar gwamnan jihar Zamfara ce ta wakilci Oluremi Tinubu yayin rabon kudin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matar Tinubu ta raba N50m a Zamfara
Matar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta raba kudi N50,000 ga mata domin bunkasa sana'a a jihar Zamfara.
Tribune ta wallafa cewa mata guda 1,000 ne suka samu kyautar kuma kowace daya ta samu N50,000 daga cikin N50m.
Dalilin rabawa mata miliyoyi a Zamfara
Matar gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Hurriya Dauda Lawal ta ce an raba kudin ne domin a tallafi mata masu kananan sana'o'i.
Hajiya Hurriya ta ce ƙananan sana'o'i ne kashin bayan tattalin arziki saboda haka tallafa musu zai taimaka wa tattali.
Matar Tinubu za ta yi rabo a sauran jihohi
Matar shugaban kasar ta bayyana cewa tallafin kudin na cikin kokarin da gwamnatin Tinubu take yi kuma za a zagaya dukkan jihohin Najeriya.
Oluremi Tinubu ta bayyana cewa a zuwa yanzu mata 70,000 ne suka ci moriyar shirin a fadin Najeriya.
An kaddamar da ba mata tallafi a Borno
A wani rahoton, kun ji cewa matar shugaban kasar Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ta kaddamar da shirin ba da tallafi ga mata a jihar Borno.
Uwargidar Najeriyar ta samu wakilcin matar mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Kashim Shettima yayin kaddamar da shirin a birnin Maiduguri.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng