Bayan Tura Sojoji Sakkwato, 'Yan Arewa Sun Fara Shinshino Karshen Rashin Tsaro
- Kungiyar Arewa maso Yamma ta North West Agenda for Peace ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na son kawo karshen rashin tsaro
- Wannan na zuwa me bayan manyan jami'an sojojin kasar nan sun tare a jihar Sakkwato bisa umarnin shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Shugabannin kungiyar na ganin matakin da Tinubu ya dauka babbar alama ce ta cewa da gaske ake shirin kawo karshen rashin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto - Kungiyar North West Agenda for Peace (NOWAP) ta bayyana fatan gwamnatin tarayya za ta kawo karshen matsalar tsaro.
Shugaban kungiyar, Abba Gana Abba da Sakatare Janar Usman Abubakar ne su ka bayyana haka a sanarwar da su ka sanya wa hannu.
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa shugabannin biyu na ganin matakin da shugaba Bola Tinubu ya dauko na umartar jami'an tsaro su tare a Sakkwato babbar alama ce.
"Tinubu zai magance rashin tsaro," NOWAP
Kungiyar NOWAP ta bayyana jin dadin yadda shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan aikin ta'addancin da ke gudana a Arewa maso Yamma.
Shugabannin kungiyar na ganin komawar kusoshin rundunar sojan kasar nan zuwa Sakkwato hanya ce ta kawo karshen matsalar da ke kara ta'azzara.
NOWAP ta koka kan rashin tsaro
Shugaban kungiyar NOWAP, Abba Gana Abba da sakatare janar dinsa, Usman sun Abubakar sun bayyana takaicin yadda rashin tsaro ya yi katutu a Arewa maso Yamma.
Kungiyar ta ce lamarin ya yi lalacewar da har ta kai jihohi hudu a shiyyar su ne kan gaba a cikin jerin jihohin kasar nan biyar da ake satar mutane.
Rashin tsaro: Sojoji sun sauka a Sakkwato
A wani labarin, mun ruwaito yadda manyan sojojin kasar nan karkashin jagorancin karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle suka sauka a jihar Sakkwato.
Wannan umarni ne na shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, inda ya bukace su da tabbatar da jami'an tsaro sun kakkabe ayyukan yan ta'adda da ta'addancin a Arewa maso Yamma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng