Bayan Tashin Farashin Fetur, Naira Ta Sake Shiga Matsala a Kasuwar Canji a Najeriya
- Yayin da ake kuka kan tsadar man fetur, darajar Naira ta ƙara faɗowa ƙasa a kasuwar hada-hadar canji ta gwamnati
- Alkaluman kasuwar NAFEM sun ce Dalar Amurka ta tashi zuwa N1,639.41 a ranar Alhamis sabanin N1,606 na ranar Laraba
- Haka nan kuma Naira ta kuma faɗuwa a kasuwar bayan fage, wani ɗan canji ya shaidawa Legit Hausa Dala ta kai N1,650
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Darajar Naira ta ƙara faɗuwa a kasuwar hada-hadar musayar kudin ƙasashen ketare da ke ƙarƙashin kulawar gwamnatin Najeriya.
Bayanai sun nuna ƙimar kudin Najeriya ta ragu zuwa N1,639.41/1$ a farashin gwamnati jiya Alhamis, 5 ga watan Satumba, 2024.
Darajar Dalar Amurka ta karu a NAFEM
Kamar yadda Daily Trust ta tattaro, ƙimar Naira ta ragu da N34 a jiya Alhamis idan aka kwatanta da farashin da aka yi cinikin kowace Dala N1,606 ranar Laraba.
Kasuwar musayar kudi ta Najeriya mai zaman kanta (NAFEM) ita ce ta tabbatar da tashin Dala ranar Alhamis.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da farashin man fetur ya ƙara tashi har a gidajen man kamfanin mai na kasa NNPCL
Dala ta tashi a kasuwar bayan fage
Haka zalika rahotanni sun bayyana cewa Naira ta ƙara faɗuwa a kasuwar bayan fage ta ƴan canji, inda Dala ta ƙara tsada zuwa N1,645 inji rahoton Vanguard.
Naira ta yi ƙasa da N5 a kan Dala, inda aka yi musaya a farashin da bai gaza N1,645/$1, ba sabanin N1,640 na ranar da ta gabata watau Laraba ba.
Wani ɗan canji da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa Legit Hausa cewa Naira ta ƙara faɗuwa a jiya Ahamis.
A cewarsa, kafin su tashi kasuwa sai da farashin Dalar Amurka ya haura N1,650 saɓanin ranar Laraba da aka yi musaya a tsakanin N1,630 zuwa N1,640.
"Maganar gaskiya farashin Dala ya wuce N1,645, zan iya cewa dai daga nan ya fara amma kafin mu tashi sai da Dala ta haura N1,650," in ji shi.
Najeriya ta hau matsayi na 3 a cin bashi
A wani rahoton kuma, an ji Najeriya ta ci gaba da runtumo bashi daga bankin duniya a mulkin Bola Tinubu duk da cire tallafin man fetur.
A rahoton kuɗi na bankin duniya, Najeriya ta haura zuwa mataki na uku a jerin kasashen da suka fi cin bashin IDA a shekarar 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng