'Yan Bindiga Sun Koma Bautar da Mutane a Gonaki Arewacin Najeriya

'Yan Bindiga Sun Koma Bautar da Mutane a Gonaki Arewacin Najeriya

  • Al'ummar karamar hukumar Shiroro a jihar Neja sun koka kan yadda yan bindiga suka mayar da su kamar bayi suna yi musu aiki a gona
  • Wani mazaunin yankin Allawa ya bayyana yadda yan bindiga da yan ta'adda suka kwace amfanin gona mai tarin yawa hannun mutane
  • Hakan na zuwa ne bayan zargin janye jami'an tsaro a yankin a wata uku da suka wuce ba tare da dawowa da su ba duk da kira da aka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Al'ummar jihar Niger sun koka kan yadda yan bindiga suka fitine su ta hanyar saka su ayyukan noma.

Sakataren kungiyar cigaban karamar hukumar Shiroro, Saidu Salihu ya buƙaci gwamnati ta kawo musu dauki.

Kara karanta wannan

Yadda ake zargin yunwa na kashe fursunoni a gidajen yarin Najeriya

Niger
Yan bindiga na saka mutane aikatau a Neja. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wani dan bindiga ya kwace buhunan waken suya da dama a hannun mutanen yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Neja: 'Yan bindiga na bautar da mutane

Wasu mazauna yankunan karamar hukumar Shiroro a jihar Neja sun nuna takaici kan yadda yan bindiga ke tilasta musu yin aikin bauta.

An ruwaito cewa yan bindiga na sanya mutane dole su yi musu noma bayan kwace musu amfanin gona da suke yi.

Mutanen Shiroro sun buƙaci taimako

Sakataren kungiyar cigaban Shiroro, Saidu Salihu ya bukaci gwamnati ta dawo da sojojin da suka tafi daga yankin domin fatattakar yan ta'addar.

Saidu Salihu ya ce yanzu yan bindiga ne suke cin karensu ba babbaka a yankin wajen cin zarafin al'umma.

Abuja za ta fuskanci barazana daga Shiroro

Sahara Reporters ta wallafa cewa wani mazaunin yankin ya ce kasancewar suna kusa da Abuja, yan bindigar za su iya tunkarar birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Tsohon dan sanda ya fallasa dalilin gaza kama yan bindiga masu kira ta waya

Saboda haka ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki matakin gaggawa wajen ganin ta samar da tsaro a Shiroro domin kaucewa yaɗuwarsa.

'Yan bindiga sun sace jigon PDP a Oyo

A wani rahoton, kun ji cewa wasu yan bindiga da ke kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kutsa a gidan jigon PDP a jihar Oyo.

An ruwaito cewa miyagun sun shiga gidan Cif Benedict Akika inda su ka rika yi wa jama'ar gidan barazanar harbe su idan su ka ce uffan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng