‘Ba Za Mu Iya Rayuwa Haka ba,’ An Hada Kai, An Yi Rubdugu ga Tinubu kan Kudin Mai
- Karin kudin man fetur na cigaba da jawo suka ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu musamman daga talakawa da jam'iyyun adawa
- 'Yan majalisun tarayya sun bukaci gwamnatin Tinubu ta dawo da farashin man fetur yadda yake domin saukakawa al'umma
- Legit ta tattauna da wani mai aikin Keke NAPEP a jihar Gombe, Saidu Magaji domin jin yadda tsadar mai ke shafan aikinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya na cigaba da shan kakkausar suka kan karin kudin man fetur da aka samu cikin makon nan.
'Dan majalisar tarayya, Alhassan Ado Doguwa ya yi kira ga gwamnati kan rage kudin man fetur amma abin ya gagara.
Jaridar Vanguard ta tatttara rahoto kan yadda aka yi rubdugu ga Bola Tinubu kan karin kudin man fetur.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta bukaci a rage kudin mai
'Dan majalisa mai lura da kwamitin fetur, Alhassan Ado Doguwa ya bukaci gwamnatin tarayya ta duba halin da ake ciki ta rage kudin mai.
Haka zalika shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Kingsley Chinda ya ce babu hikima cikin kara kudin mai alhali ana cikin wahala.
PDP da NNPP sun nemi a rage kudin mai
Sakataren yada labaran PDP, Dabo Ologunagba ya ce yan Najeriya ba za su iya rayuwa da karin kudin ma fetur ba, saboda haka ya bukaci Tinubu ya gaggauta rage kudin.
A daya bangaren, sakataren yada labaran NNPP, Ladipo Johnson ya ce APC na son jefa yan Najeriya cikin mummunan talauci saboda karin kudin mai.
Kungiyoyi sun huro wuta kan kudin mai
The Guardian ta wallafa cewa kungiyar CNG a Arewacin Najeriya ta yi Allah wadai da karin kudin mai da aka yi, ta kuma buƙaci a rage kudin cikin gaggawa.
Haka zalika kungiyar lauyoyi ta ta kasa, NBA ta ce karin kudin mai zai kara saka mutane a wahala ta inda dukkan abubuwa za su tashi a Najeriya.
Legit ta tattauna da me Keke NAPEP
Wani me aikin keke NAPEP a jihar Gombe, Saidu Magaji ya ce abin da kungiyoyin suka yi abin a yaba ne kasancewar lamura sun rincabe.
Saidu Magaji ya ce yanzu haka da kyar suke samun na cefane saboda tsadar man fetur da ya ke shafan aikisu, saboda haka ya ce za su yi farin ciki idan aka rage farashin mai.
An yi zanga zangar kudin mai a Kwara
A wani rahoton, kun ji cewa yan acaba da masu aikin Keke NAPEP sun yi zazzafan zanga zanga kan ƙarin kudin mai da aka yi a faɗin Najeriya.
Zanga zangar ta faru ne yankunan Maraba, Taiwo, Isale da sauran wurare a jihar Kwara domin nuna kin amincewa da karin kudin mai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng