Zanga Zanga Ta Barke kan Karin Kuɗin Fetur, an Rufe Gidajen Mai da Shaguna

Zanga Zanga Ta Barke kan Karin Kuɗin Fetur, an Rufe Gidajen Mai da Shaguna

  • Yau Alhamis yan acaba da masu aikin Keke NAPEP sun yi zazzafan zanga zanga kan ƙarin kudin mai da aka yi a faɗin Najeriya
  • Zanga zangar ta faru ne yankunan Maraba, Taiwo, Isale da sauran wurare a jihar Kwara domin nuna kin amincewa da karin kudin mai
  • Legit ta tattauna da wani dan acaba a jihar Gombe kan halin da suka shiga a kan wahalar man fetur da kara masa kudi da aka yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara - Zanga zanga ta barke a jihar Kwara domin nuna kin amincewa da karin kudin mai da aka yi a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Kowa ya shirya sake fita zanga zanga": Ministan Buhari ya soki malamai

Masu sana'ar acaɓa da Keke NAPEP ne suka yi zanga zanga tare da daina daukan mutane a yau Alhamis.

Kwara
Masu abubuwan hawa sun yi zanga zanga a Kwara. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa wasu shagunan da ake sayayya sun kulle yayin da aka fara zanga zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi zanga zangar kudin mai a Kwara

Rahotanni da suka fito daga jihar Kwara sun nuna cewa masu acaɓa da Keke NAPEP sun nuna fushi kan karin kudin mai.

Masu abubuwan hawan sun fito ta wajen shatale-talen Unity Garaje, Offa Garaje, Maraba, Taiwo domin yin zanga zanga.

Cikin abin da suka yi domin nuna bakin ciki sun daina daukan mutane domin kai su wajen aiki da harkokin yau da kullum.

Halin da aka shiga yayin zanga zanga

Rahotanni sun nuna mutane sun dawo tafiyar kafa yayin da masu abubuwan hawa suka daina daukarsu zuwa wajen da za su je.

Kara karanta wannan

Yadda ake zargin yunwa na kashe fursunoni a gidajen yarin Najeriya

Tribune ta ruwaito cewa an rufe gidajen mai yayin zanga zangar domin jin tsoron kar miyagu su afka musu yayin da ake zanga zangar.

Haka zalika masu sayar da abubuwa a shagunan Ilorin sun kulle saboda jin tsoron kar lamarin ya rikice azo a musu mummunar sata.

Legit ta tattauna da dan acaba

Wani dan acaba a jihar Gombe, Ibrahim Musa ya zantawa Legit cewa a hallin yanzu ba sosai suke samun riba ba saboda tsadar man fetur.

Ibrahim Musa ya ce har yanzu ba su yi magana a kungiyance kan fita zanga zanga ba amma idan aka shirya fita zai zama na gaba gaba.

Farashin mai: Dangote ya magantu

A wani rahoton, kun ji cewa Aliko Dangote ya yi magana kan zancen da ake yaɗawa zai rika sayar da litar man fetur a kan N897 a Najeriya.

Matatar Dangote ta ce har yanzu tana kan tattaunawa da kamfanin NNPCL domin fitar da farashin man fetur da za ta rika kai wa kasuwa.

Kara karanta wannan

Matasa sun barke da zanga zanga kan ƙarin kudin man fetur, sun toshe hanyoyi

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng