Tsohon Minista Ya Roki Sufeton Yan Sanda Ya Gaggauta Cafke Nyesom Wike
- Jagoran yan kabilar Ijaw a Najeriya, Edwin Clark ya umarci shugaban yan sandan Najeriya da ya gaggauta cafke ministan Abuja
- Edwin Clark ya ce ministan harkokin Abuja ya cancanci a kama shi saboda kalaman tayar da hankali da ya yi a wajen taro
- Wike ya ce zai tayar da hankali ne a jihohin PDP yayin wani taron jam'iyyar a birnin Fatakwal a ranar Lahadi da ta gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Daya daga cikin manyan jagororin ƙabilar Ijaw, Cif Edwin Clark ya bukaci sufeton yan sanda ya gaggauta kama ministan Abuja, Nyesom Wike.
Edwin Clark ya ce Nyesom Wike ya aikata babban laifi a kan wasu kalamai da ya fada a wani taro a Fatakwal.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Cif Edwin Clark ya ba sufeton yan sanda umarnin ne a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Wike ya fada a Fatakwal?
A ranar Lahadi da ta wuce ne ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce zai kunna wutar rikici a jihohin da PDP ke mulki a Najeriya.
Nyesom Wike ya fadi haka ne yayin da rikicin jami'yyar PDP ya yi ƙamari musamman tsakaninsa da gwamna Fubara.
Clark ya bukaci a cafke Wike
Edwin Clark ya ce ya yi kira ga sufeton yan sanda, IGP Kayode Egbetokun a kan ya kama Nyesom Wike kan kalaman tayar da fitina da ya yi.
Clark ya ce irin kalaman ne wasu yan Najeriya suka yi aka kama su saboda haka Wike ma ya cancanci kamu.
Wike bai kyauta wa Tinubu ba inji Clark
Edwin Clark ya ce kalaman da Nyesom Wike ya yi za su jawo raini ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Vanguard ta wallafa cewa a kan haka ne Clark ya ce ya idan aka kama Nyesom Wike ya zama dole a sanya shi ya tuba daga abin da ya fada.
NUF ta yi Allah wadai da kalaman Wike
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar NUF ta Arewa maso Gabas ta yi Allah wadai da abin da Ministan Abuja ya yi wanda ta kira da dabancin siyasa.
Ƙungiyar ta ce barazanar da Nyesom Wike ya yi wa gwamnonin PDP kwanan nan ta tona asirin munanan ɗabi'unsa da rashin ladabi da yake da shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng