N897: Dangote Ya Fadi Gaskiya kan Farashin Litar Man Fetur a Matatarsa

N897: Dangote Ya Fadi Gaskiya kan Farashin Litar Man Fetur a Matatarsa

  • Alhaji Aliko Dangote ya yi magana kan zancen da ake yaɗawa wai zai rika sayar da litar man fetur a kan N897 a Najeriya
  • Matatar Dangote ta ce har yanzu tana kan tattaunawa da kamfanin NNPCL domin fitar da farashin man fetur da za ta rika tacewa
  • Kamfanin ya yi kira na musamman ga yan Najeriya kan yin bincike kafin yarda da wani labari da za a rika yaɗawa a duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Alhaji Aliko Dangote ya yi bayani kan yadda farashin man fetur zai kasance a matatarsa.

Dangote ya yi magana ne bayan an fitar da wani farashi da aka ce kamfanin ne ya sanar da yadda zai rika sayar da mai.

Kara karanta wannan

Tsohon Minista ya roki Sufeton 'Yan sanda ya gaggauta cafke Nyesom Wike

Dangote
Dangote ya yi magana kan farashin man fetur. Hoto: Dangote Industries
Asali: UGC

Legit ta tatttaro bayanan da Dangote ya yi a kan farashin ne a cikin wani sako da shafin Dangote Industries ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote ya fara sayar da mai a N897?

Dangote ya ce wata jarida (Ba Legit ba) ta wallafa labarin cewa ya fara sayar da litar man fetur a kan N897 a Najeriya.

Kamfanin ya ce labarin nan ya fita ne a ranar Laraba amma kuma babu kamshin gaskiya a cikinsa kwata kwata.

Yaushe Dangote zai fitar da farashin mai?

Alhaji Aliko Dangote ya ce a yanzu haka bai kammala tattaunawa da kamfanin NNPCL ba kan yadda farashin mai zai kasance a matatarsa.

Dangote ya ce farashin man fetur abu ne da ba mutum daya ba ne zai yanke, ya ce sai masu ruwa da tsaki, gwamnati da yan kasuwa sun zauna.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fadi hanyar da za a taimakawa gwamnatin Tinubu

Dangote ya yi kira ga 'yan Najeriya

Dangote ya ce yana da tabbas a kan cewa zai samar da ingantaccen mai kuma wadatacce ga yan Najeriya daga matatarsa.

Sai dai ya yi kira ga al'umma kan kaucewa jita jita da za a rika yaɗawa kan farashin man fetur dinsa da sauran abubuwa.

Adadin man da Dangote zai samar

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matatar man Dangote za ta rika samar da lita miliyan 25 na fetur a kullum a Satumba.

Hukumar da ke sa ido kan harkokin man Najeriya (NMDPRA) ta ce matatar Dangote za ta kara yawan litar zuwa miliyan 30 a watan Oktoba mai zuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng