Sanata Ndume Ya Bukaci Sojoji Su Kawo Ƙarshen 'Yan Ta'addan Boko Haram
- Muhammad Ali Ndume ya nuna damuwarsa kan yadda ƴan ta'addan Boko Haram ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a Najeriya
- Sanatan na Borno ta Kudu ya buƙaci sojoji su ƙara ƙaimi wajen murƙushe ƴan ta'addan da ke a dajin Sambisa da tsaunin Mandara
- Ndume ya bayyana cewa hare-haren ƴan ta'addan na kawo koma baya ga manoman da suka koma gidajensu a yankin Gwoza
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Sanata Muhammad Ali Ndume ya buƙaci dakarun sojojin Najeriya su ƙara ƙaimi wajen fatattakar ƴan ta'addan Boko Haram.
Ali Ndume ya buƙaci sojoji na Operation Hadin Kai da su ƙara ƙoƙarin da suke yi wajen murƙushe ragowar ƴan ta'addan da ke ɓoye a dajin Sambisa da tsaunin Mandara da ƙauyukan da ke tsakanin Gwoza da Kamaru.
Ndume ya koka kan ayyukan ƴan ta'adda
Sanata Ndume ya bayyana cewa hare-haren ƴan ta'addan suna kawo koma baya ga manoman da suka koma gidajensu a Ngoshe, Kirawa, Warabe, Wala, Pulka, da Gwoza, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun koma satar amfanin gona wanda bai isa yi ba, ba tare da fuskantar wata tangarɗa ba, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
"Ƙaruwar hare-haren ƴan ta'adda ya zama babbar matsala ga manomanmu waɗanda suka koma ƙauyukansu. Ƴan ta'addan na ci gaba sace amfanin gonansu ba tare da wata tangarɗa ba."
- Sanata Ali Ndume
Sanata Ndume ya roƙi sojoji da jami'an tsaro su ƙara ƙaimi wajen ƙoƙarin da suke yi domin murƙushe ragowar ƴan ta'addan Boko Haram da ke ɓoye a dajin Sambisa da tsaunin Mandara.
Gwamnonin Arewa sun magantu kan harin Yobe
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewa kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, ya yi Allah wadai da harin da ƴan ta'adda suka kai a jihar Yobe.
Gwamna Inuwa ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aka yi asarar rayuka da dama a ƙauyen Mafa da ke ƙaramar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe sakamakon harin na ƴan ta'adda.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng