Najeriya Ta Zama Ƙasa Ta 3 da Ta Fi Yawan Karɓo Bashin Bankin Duniya a 2024

Najeriya Ta Zama Ƙasa Ta 3 da Ta Fi Yawan Karɓo Bashin Bankin Duniya a 2024

  • Najeriya ta ci gaba da runtumo bashi daga bankin duniya a mulkin Bola Ahmed Tinubu duk da cire tallafin man fetur
  • A rahoton kuɗi na bankin duniya, Najeriya ta haura zuwa mataki na uku a jerin kasashen da suka fi cin bashin IDA a 2024
  • Alkaluman sun nuna ta ƙara yawan bashin da take ƙarɓowa da 14.4% kwatankwacin $2.2bn daga Yuli, 2023 -Yuni 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Yayin da ake fama da tsadar rayuwa, Najeriya ta matsa zuwa mataki na uku a jerin ƙasashen da suka ci bashin bankin duniya.

Alkaluman sun nuna cewa zuwa ranar 30 ga watan Yuni, 2024, Najeriya ta ɗare mataki na uku a ƙasashen da bashin bankin duniya na IDA ya yi wa katutu.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya shiga matsala bayan ya yi wa wasu gwamnoni barazana

Bola Tinubu.
Najeriya ta matsa daga matsayi na 4 zuwa na 3 a jerin kasashen da suka fi karɓo bashin bankin duniya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Nairametrics ta ce a rahoton kuɗi na bankin duniya, adadin bashin da Najeriya ke runtumowa daga IDA ya ƙaru da kaso 14.4% a shekarar na muke ciki ta 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya ta ƙaro bashin bankin duniya

Rahoton ya nuna cewa yawan rancen da gwamnatin Najeriya ta karɓo daga bankin duniya ya tashi daga $14.3bn a 2023 zuwa $16.5bn a 2024.

Wannan ƙarin na Dala biliyan 2.2 ya sa Najeriya ta hau matsayi na uku a jerin ƙasashen da suka fi runtumo bashi daga IDA na bankin duniya.

Najeriya ta tashi daga matsayinta na ƙasa ta huɗu da tafi yawan karɓo bashi a shekarar 2024.

Tinubu ya ci bashin akalla $2.2bn

Shekarar da ake lissafi a kanta ta kama ne daga watan Yuli 2023 zuwa watan Yuni 2024, wanda ke nufin Najeriya ta karbi akalla Dala biliyan 2.2 daga bankin duniya karkashin gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

TUC ta yi fatali da ƙarin farashin man fetur, ta aika sakon gaggawa ga Bola Tinubu

Bayanai sun nuna wannan tulin bashin ya banbanta da lamunin raya ƙasa (IBRD) wanda shi ma daga bankin duniya ake karɓo shi, rahoton Punch.

NEC ta yi zama a Aso Rock

A wani rahoton kuma, an ji Kashim Shettima ya jagoranci taron majalisar tattalin arziki NEC a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Bayanai sun nuna Aliko Ɗangote da attajitin nan na kasar Amurka, Bill Gates sun halarci taron wanda ya gudana ranar Laraba, 4 ga watan Satumba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262