Gwamnan Arewa Zai Tura ’Ya ’yan Talakawa Karatu Kasar Waje

Gwamnan Arewa Zai Tura ’Ya ’yan Talakawa Karatu Kasar Waje

  • Gwamnatin Katsina ta fitar da sanarwa kan shirin kai yan asalin jihar karatu kasar waje domin inganta harkokin ilimi
  • Mataimakin gwamnan jihar Katsina, Faruk Lawal Jobe ne ya bayyana haka inda ya ce daliban za su tafi ne ranar 13 ga Satumba
  • Faruk Lawal Jobe ya bayyana cewa hakan na cikin kokarin gwamnatin jihar kan ganin al'umma sun samu ilimi mai inganci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta kammala shirye shiryen kai ɗalibai yan asalin jihar karatu a kasar waje.

Mataimakin gwamnan jihar ya ce sun biya kudin karatu da sauran abubuwa ga dukkan daliban na tsawon lokacin da za su yi karatun.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fadi hanyar da za a taimakawa gwamnatin Tinubu

Gwamna Radda
Gwamna Radda zai kai dalibai karatu kasar Sin. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Legit ta samu bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da jami'in yada labaran gwamnatin Katsina, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalibai nawa za a kai karatu a Katsina?

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa za ta fitar da dalibai yan asalin jihar guda 68 ne domin karatu a kasar Sin a ranar 13 ga Satumba.

Faruk Lawal Jobe ya ce daliban za su karanci fasahar zamani da harkar tattalin arziki ne a kasar Sin.

Yadda aka zabo 'ya'yan talakawa a Katsina

Gwamnatin Katsina ta bayyana cewa an zaɓo daliban ne daga makarantun gwamnatin jihar kuma daga gidajen marasa karfi.

Haka zalika gwamnatin ta yi karin haske kan cewa an zakulo daliban ne cikin dukkan kananan hukumomin jihar 34.

Ƙoƙarin inganta ilimi a Katsina

Faruk Lawal Jobe ya ce tura dalibai kasar waje na cikin kokarin gwamnatin Dikko Umaru Radda na ganin an inganta ilimi a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Gida Gida ya fusata da aiki, ya kwace kwangilar titi a Kano

Mataimakin gwamnan ya ce a kwanakin baya gwamnatin ta tura dalibai 41 domin karatun likita kasar Misra.

Jigawa: Za a kai dalibai karatu waje

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Jigawa ya bayyana shirin dawo da kai dalibai yan asalin jihar karatu a kasar waje domin bunkasa ilimi.

Rahotanni sun nuna cewa majalisar zartarwar jihar ta amince da dawowa da shirin bayan tsaiko da ya samu na shekarun da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng