Gwamma Ya Kafa Kwamiti, Zai Fara Biyan Sabon Mafi Karancin Albashi Na N70,000

Gwamma Ya Kafa Kwamiti, Zai Fara Biyan Sabon Mafi Karancin Albashi Na N70,000

  • Gwamnan jihar Borno ya amince da sabon mafi karancin albashi na N70,000, ya kafa kwamitin da zai duba yadda za a aiwatar da dokar
  • Sakataren gwamnan jihar Borno, Bukar Tijjani ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Maiduguri
  • Tijjani ya ce kwamitin zai yi nazari kan tsarin da tarayya ta bi wajen ƙarin albashin tare da tantance yadda za a aiwatar a Borno

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Gwamna Babagana Zulum na Borno ya amince da kafa kwamitin mutane 12 domin aiwatar da dokar sabon mafi karancin albashi na N70,000.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bukar Tijani, sakataren gwamnatin jihar (SSG) ya fitar ranar Laraba a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Nenadi Usman: An naɗa mace a matsayin shugabar jam'iyya ta ƙasa a Najeriya

Gwamna Babagana Zulum.
Gwamnatin Borno ta kafa kwamitin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi Hoto: Prof. Babagana Umaru Zulum
Asali: Facebook

Gwamna Zulum na shirin biyan N70,000

A cewar sanarwar, kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na jihar Borno, Babagana Mallumbe, shi ne zai jagoranci kwamitin, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai kuma shugaban hukumar kula da ma'aikata, Mallam Fannami, a matsayin wanda zai yi aiki tare da shugaban kwamitin aiwatar da sabon albashin.

Sanarawar ta kuma bayyana babban sakataren ma'aikatar ƙaddamarwa, Sadiq Mohammed a matsayin sakataren kwamitin, rahoton Daily Post.

Wane aiki gwamna ya ɗorawa kwamitin?

A cewar sanarwan, ana sa ran kwamitin zai yi nazari a kan yadda tsarin albashin yake a matakin tarayya tare da tantance hanyar da za aiwatar da shi a Borno.

"Tsarin ƙarin albashin da aka yi a matakin tarayya zai zama madubi wajen tantance gyara da ƙarin albashin za a yi wa ma'aikatan gwamnati a nan jihar Borno," in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

Gobara ta lakume sashen babban asibiti a Arewa, gwamna zai dauki mataki

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rawaito cewa Antoni Janar kuma kwamishinam shari'a na jihar Borno na cikin 'yan kwamitin.

Sauran ƴan kwamitin sun haɗa kungiyar kwadago NLC da takwararta TUC ta reshen Borno da sauran masu ruwa da tsaki a biyan albashin ma'aikata.

Gwamnan Ebonyi zai yi karin albashi

A wani rahoton kun ji cewa yayin da ake fama da tashin farashin fetur, gwamnan jihar Ebonyi ya amince da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Gwamna Francis Nwifuru ya yi bayanin cewa sabon albashin ba yana nufin kowane ma'aikaci zai samu ƙarin N70,000 a albashinsa ba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262