“Babu Wahala a Mulkin Najeriya”: Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Matsalolin Kasar

“Babu Wahala a Mulkin Najeriya”: Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Matsalolin Kasar

  • Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce babu wata wahala a mulkin Najeriya kamar yadda ake tunani
  • Obasanjo ya ce ba kamar yadda ake zato ba Najeriya tana da sauki mulki kawai an rasa shugabanni ne da suka dace
  • Tsohon shugaban ya ce idan har ana neman cigaba to dole shugabanni su sauya salon da suke mulki a kasar nan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi magana kan matsalolin da ake fuskanta a Najeriya.

Obasanjo ya ce babu wata wahala a mulkin Najeriya kamar yadda ake tunani illa rashin shugabanci.

Obasanjo ya fadi matsalolin da Najeriya ke fuskanta
Cif Olusegun Obasanjo ya ce babu wahala a mulkin Najeriya. Hoto: Olusegun Obasanjo.
Asali: Facebook

Obasanjo ya fadi manyan matsalolin Najeriya

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban kasa ya shiga taron NEC da manyan attajirai 2, bayanai sun fito

Daily Trust ta ce tsohon shugaban kasar ya fadi haka ne a wani lakca a yau Laraba 4 ga watan Satumbar 2024 a Lagos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obasanjo ya ce babbar matsalar da kasar ke fuskanta bai wuce rashin ingantaccen shugabanci ba.

Tsohon shugaban kasar ya ce tabbas akwai kalubale a Najariya amma ya ce babbar hanyar samun cigaba shi ne shugabannin nagari, cewar rahoton Punch.

Obasanjo ya fadi nasarorin da ya kawo

"Na sha fada Najeriya tana kalubale amma ya kamata ku fahimta ba ta da wahalar mulka, ya kamata kowa ya yi gaskiya da kansa da ubangiji da kuma kasarsa."
"Lokacin da nake mulki, na yi duk mai yiwuwa domin kasa ta kuma har yanzu zan bugi kirji a kan haka."

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya ce a lokacin mulkinsa ya yi amfani da karancin kudi da kasar ke da shi inda ya kawo cigaba mai matukar yawa.

Kara karanta wannan

"Muna son sauyi": An ba Atiku, Tinubu da Peter Obi shawara kan sake takara a 2027

Obasanjo ya ja kunnen shugabanni

Kun ji cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce za a samu matsala mai girma idan shugabannin Afirka ba su magance matsalolinsu ba.

Cif Obasanjo ya ce wannan fatara da talaucin da al'umma ke ciki a nahiyar Afirka ba kaddara ba ce daga Allah, wasu mutane ne suka jawo matsalolin.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce idan aka duba ɗumbin albarkatun da Allah ya jibge a nahiyar Afirka, babu dalilin da da zai sa talauci ya yiwa mutane katutu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.