“Ku Kuka Yaudari ’Yan Kasa ba Tinubu ba”: An Caccaki NLC bayan Kara Kudin Fetur

“Ku Kuka Yaudari ’Yan Kasa ba Tinubu ba”: An Caccaki NLC bayan Kara Kudin Fetur

  • Kungiyar The Citizens for Democratic Dividends ta caccaki shugaban NLC, Joe Ajaero kan sukar Bola Tinubu game da farashin mai
  • Kungiyar ta ce Ajaero kan shi kawai ya sani ba wai ta yan Najeriya yake yi ba inda ta ce shi ya yaudari yan kasar kan karin albashi
  • Wannan na zuwa ne bayan jagoran kwadagon ya zargi Tinubu da yaudara kan yarjejeniyar da suka yi kan kara farashin man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Wata kungiya a Najeriya ta caccaki NLC kan sukar Bola Tinubu game da karin farashin fetur.

Kungiyar mai suna The Citizens for Democratic Dividends ta ce NLC ce ta yaudari 'yan Najeriya ba Tinubu ba.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fadi hanyar da za a taimakawa gwamnatin Tinubu

An soki kungiyar NLC kan zargin Tinubu da yaudara
Kungiya ta caccaki NLC kan yaudarar 'yan Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nigeria Labour Congress.
Asali: Facebook

Kungiya ta soki NLC kan caccakar Tinubu

Babban daraktan kungiyar, Ahmad Idris shi ya bayyana haka a yau Laraba 4 ga watan Satumbar 2024, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idris ya ce kungiyar NLC da shugabanninta gina kansu suke yi a madadin nemawa yan Najeriya hakkokinsu.

"Lokacin da yan Najeriya suke shan wahala da kiran zanga-zanga, NLC sun kawar da kansu kan lamarin inda suka mayar da hankali kan mafi karancin albashi."
"Yanzu da ake zarginsa kan kifar da gwamnati, Ajaero yana neman saka yan Najeriya a cikin matsalarsa."

- Ahmad Idris

NLC ta fadi yaudararta da Tinubu ya yi

Wannan na zuwa ne bayan NLC ta zargi Tinubu da yaudararsu bayan yarjejeniyar da suka yi kan karin farashin mai.

Shugaban kungiyar, Joe Ajaero ya ce sun tsayar da matsaya kan Tinubu ba zai kara kudin ba idan suka amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Kungiyar NTCA ta ce Tinubu zai zarce a 2027, ta ba 'yan Najeriya mafita

NNPCL ta kara farashin man fetur

A wani labarin, kun ji cewa Kamfanin mai na NNPCL ya kara farashin litar mai a mafi yawan wurare a fadin Najeriya.

A mafi yawan gidajen mai musamman na kamfanin NNPCL, an kara kuɗin har zuwa N855 kan farashin lita da a baya ake siyarwa N568.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu gidajen mai na musamman na NNPCL suna siyar da litar har N897 daga N568 a baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.