"Shi Ya Rusa Mu": Fitaccen Dan Kasuwa Ya Fadi Illar da Yar'Adua Ya Yi Masa da Dangote
- Shahararren dan kasuwa, Femi Otedola ya koka kan yadda gwamnatin marigayi Umaru Yar'Adua ta dakile shi da Aliko Dangote
- Odetola ya bayyana cewa sun shirya mallakar matatun mai a Kaduna da Port Harcourt amma shugaba Yar'Adua ya rusa tsarin
- Ya ce sun kulla yarjejeniya na siyan hannun jari a matatun biyu a mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo kafin ya sauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Fitaccen dan kasuwa, Femi Otedola ya fadi yadda marigayi Umaru Musa Yar'Adua ya dakile su da Aliko Dangote.
Otedola ya ce gwamnatin marigayi Ƴar’Adua ta yi musu makarkashiya shi da Aliko Dangote kan mallakar matatun mai a Kaduna da Port Harcourt.
Yadda Yar'Adua ya rusa shirin Dangote, Otedola
Dan kasuwar ya ce sun sayi hannun jari a matatun biyu daga Gwamnatin Tarayya a ƙarshen mulkin Olusegun Obasanjo, cewar rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Otedola ya ce sai dai sun samu tasgaro daga gwamnatin marigayi Umaru Musa Yar'Adua ta rusa wannan tsarin ba tare da bata lokaci ba.
Fitaccen dan kasuwar ya ce a lokacin a shirye suke su kawo sauyi tare da dawo da martabar matatun man guda biyu.
Otedola ya fadi shirinsu na mallakar matatun mai
”Gwamnatin Ƴar’Adua ta dakile yarjejeniyar mallakar matatun man da muka yi a karshen mulkin Obasanjo da ni da Dangote."
"Sai dai kuma da yake akwai abin da Allah ya shirya wa Ɗangote, ga shi yanzu ya mallaki abin da ya fi wanda ya rasa."
- Femi Otedola
An tabbatar da cewa da yarjejeniyar ta kullu, Dangote da Otedola za su mallaki kaso 50 da kaso 20 na matatun kasar.
Dangote ya gindaya sharuda ga yan kasuwa
A wani labarin, kun ji cewa matatar man Aliko Dangote ta bayyana tsarin yadda za ta siyar da fetur ga 'yan kasuwa.
Matatar ta tabbatar da cewa za ta fitar man kasashen ketare idan har 'yan kasuwa daga Najeriya suka ki siyan ma da take fitarwa.
Mataimakin shugaban bangaren man da kuma gas, Devakumar Edwin ya bayyana haka a ranar 2 ga watan Satumbar 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng