Rai Ya Ɓaci: Matasa Sun yiwa Soja Jina Jina, Sun Cinnawa Mutum Wuta da Ransa
- Wasu fusattatun matasa sun cinna wuta ga wani mutum da suka zarga da hannu wajen sace babur da ake sana'ar acaba
- Bayan kashe mutumin, an ji cewa matasan sun yi wa wani soja rauni sosai, suka nemi hallaka shi kafin ya tsallake rijiya ta baya
- Rahotanni sun nuna cewa matasan sun fusata ne bayan an yawaita sace sacen abin hawa a wajen masu aikin acaɓa a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ogun - Wasu matasa masu sana'ar acaba sun cinna wuta ga wani da suka zarga da satar babur a jihar Ogun.
An ruwaito cewa matasan sun nemi hallaka wani soja wanda ya samu ya tsallake rijiya ta baya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rundunar sojan Najeriya a Ogun ta tabbatar da faruwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An cinnawa matashi wuta a jihar Ogun
Wasu masu acaba a jihar Ogun sun cinna wuta ga wani matashi da ake zargi da satar babur inda ya mutu har lahira.
An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a yankin Ilisha-Remo dake karamar hukumar Ikenne a jihar Ogun.
Matasa sun yi wa soja jina jina a Ogun
Haka zalika Jaridar Punch ta ruwaito cewa yan acaban sun afka kan wani sojan Najeriya yayin da suka kona mutumin har lahira.
Sojan ya samu ya tsallake rijiya ta baya bayan sun yi masa munanan raunuka amma kuma sun bi shi suna neman hallaka shi.
Sojoji sun kubutar da jami'insu a Ogun
Shugaban kungiyar cigaban yankin, Otunba Wemmy Osude ya ce yan acaban kusan 200 ne suka bi sojan gidan da ya buya.
Ana haka ne sai rundunar sojin Najeriya ta isa wajen kuma ta samu damar kubutar da jami'in sojan.
Kakakin rundunar sojin Najeriya na runduna ta 35, Kyaftin Idereghi Akari ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa sojan ba ɓarawo ba ne.
An kar hari karamar hukumar Anambra
A wani rahoton, kun ji cewa wasu yan bindiga kimanin 30 sun dura ƙaramar hukumar Ogbaru a Anambra inda suka bude wuta a sakatariya.
Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun yi kone kone mai muni a karamar hukumar kafin su yi musayar wuta da yan sandan jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng